Offline

A Ranar 13 December 2015, Just before a Harbe ni a Zaria.



-Malama Jummai Ahmad Karofi

Wani Saurayi Yazo zai Wuce da gudu, Ya gan ni a zaune. Sai Ya ja Ya tsaye a gaba Na. Yace da ni,  an Harbe ki ne? Saboda Ya ga jikina duk jini, Sanadiyyar Yarinya Karama da aka harba Muka dauko, Jinin ta na ta tsartuwa a jikina.

A lokaci guda Ya daga Murya Yana tambaya wa ke Kusa? Ga Wata an harba. Sai na amsa da Murya Mai rauni Nace ba a harbe ni ba. Sai Yace Malama ku tashi a nan. It is not safe Yanzu za su zo nan. Na kalle shi na ce ina ne is safe today? Nace Mashi Ya wuce Kawai Ya bar ni. 

Rufe baki na ke da Wuya Sai na ga Yayi Sama Ya fado, Mararsa ta yi fatafata. Ashe akwai Soja daga can bayanshi Ya harbo shi. Ina kallon shi a gaba na jini nata tartsatsa daga Mararsa. Ya kalle ni Yace ki taimake ni. Na ce mi zan iya yi maka? Nace Kama rigarka ka hada bakin ka daure marar, sai ka kifa ciki ka ja jikinka zuwa cikin gidan nan. Yaro mai Koqarin gaske. Ya yi yadda na gaya masa.

Ina kallon shi Yana Jan Ciki Yana Kokarin Shiga gidan, kaman ance kalli gaban ki. Ina daga kai sai na jiyo harbi a kaina ratatata haka. Sai na kwanta rubda ciki. Amma ina harbin Ya riga ya iske ni.

Post a Comment

Previous Post Next Post