" Dangane da da'irorin 'yan uwa da suke ta bazuwa a ko'ina, inda da can ba 'yan uwa yanzu akwai. Abin da za mu lura shi ne mu fa ba kungiya ba ce, mu addini ne, in muna da wata kungiya, to Musulunci ne kungiyarmu. Ba kungiya muka kafa muka nada mata Shugaba da Sakatare da Ma'aji da mai watsa labaru, da sauransu ba. Wannan tsarin ma mu bai dace da mu ba."
"Inda duk aka sami wani dan'uwa, kuma Allah ya ba shi sanin wannan addini daidai gwargwado, kuma daidai gwargwadon yana sanar da mutane abin da Allah ya sanar da shi, mutane suka kewaye shi, zance ya kare. Amma babu irin wadannan tsare-tsare na 'yan kungiya. In ya zama tsare-tsaren 'yan kungiya ne, to irin makomar da kungiyoyi suka saba fuskanta, to irin su mu ma za mu fuskanta."
"Don haka tun farkon 'Harkar nan ba mu taba cewa kungiya muka kafa ba, a'a addini ne ga shi muna karanta shi, daidai gwargwadon fahimtarmu muna aikatawa. Duk wanda yake irin wannan karatu yana aikatawa, muna tare da shi, mun san shi ko ba mu san shi ba."
Wani bangare na Jawabin da Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar mai suna Nasihohi ga masu kishin Musulunci a BUK Kano.
Tags
Quotations