_ Sayyid Zakzaky (h) - Zantukan hikima.
Ita Fikira ita ke tafiyar da rayuwar mutum, zantukan mutum da ayyukan gangar jikinsa, sakamako ne na irin tunaninsa, zuciya ke sauwalawa mutum abu, sannan ya aikata.
Wato kenan idan aka samu fikira gurvatacciya, to za a samu gurbataccen aiki, don haka in ana son kyakkyawan aiki, to dole a gina kyakkyawar fikira, don ita ce asasin kyakkyawan aiki.
_ Daga littafin Zantukan hikima na Sayyid Zakzaky (h) wallafar cibiyar Wallafa.
© Freedom Fighters Ng.
Tags
Quotations