Offline

Harin Jirgin Saman “Isra’ila” Ya Kashe Palasɗinawa 16 a Gaza, Ciki Harda Yara 10.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Akalla Falasɗinawa 16 ne suka rasa rayukansu, ciki har da yara 10, bayan wani mummunan harin jirgin sama da dakarun mamaya na “Isra’ila” suka kai kan Palasɗinawa da ke jiran agajin abinci a tsakiyar zirin Gaza, a Deir Al-Balah.

Harin ya auku ne a kusa da wurin wankin kaya na Al-Bashir, a unguwar Al-Zuwari, inda mata da yara suka hallara don samun taimakon abinci. Shaidu sun bayyana yadda aka ga gawarwakin yara da manya warwatse a kan titi.

"Sun fito ne kawai don neman abinci ga yaransu – amma sai suka zama gawawwaki,” in ji wani shaidar gani da ido.

A lokaci guda, manyan tankokin yakin “Isra’ila” sun bude wuta a kan sansanonin 'yan gudun hijira a yankin Al-Maslakh, da ke yammacin Khan Yunis, inda mutane da dama suka jikkata, yayin da sansanonin suka lalace gaba ɗaya. Da ma dai dayawan mutanen sansanin sun tsere sun tafi neman mafaka wasu wurare.

Haka nan, an samu rahoton harbi da manyan bindigu kirar "Machine Gun" daga motocin sojin “Isra’ila” a unguwar Al-Tuffah, da ke gabashin birnin Gaza. A sauran sassan gabas da kudu na birnin kuma an kai hare-hare tare da rushe  gine-gine, inda aka tarwatsa gidajen Falasɗinawa da dama.

Wannan kisan gillar ya zama wani ɓangare na jerin ta'addancin yau da kullum da dakarun mamaya ke aiwatarwa a Gaza. Duk da koke-koken kungiyoyin jin kai da masu rajin kare hakkin bil’adama, Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran manyan ƙasashe sun gaza daukar matakin dakatar da abin da ke ci gaba da zama kisan kare dangi.

A wani sabon rahoto daga Hukumar Lafiyar Mata ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA), ta bayyana damuwa matuƙa dangane da halin da mata masu juna biyu da masu shayarwa ke ciki a Gaza. A cewar UNFPA, kimanin mata 50,000 ba su ci komai ba tsawon kwanaki da dama, lamarin da ke hana su samun ƙarfi ko kuma shayar da jarirai.

“Ana haifo Jarirai kafin lokacin haihuwar su ya yi, kuma da ƙarancin nauyi,” in ji hukumar. “Yara kanana na fuskantar haɗarin mutuwa ko nakasa ta dindindin.”

Yayin da ake ci gaba da kashe rayuka da rusa gidaje, yanayin yunwa, yunƙurin kare rai, da sakacin duniya ya bar al’ummar Gaza cikin mugun hali, ba tare da taimako daga manyan ƙasashen duniya ba.


ABS Radio - Daga Gaza

Post a Comment

Previous Post Next Post