Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana a ranar Alhamis cewa an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na Ben Gurion bayan da wani makami mai linzami daga Yemen ya nufi tsakiyar Isra’ila, wanda ya haddasa jin karar jiniyar dake alamta harin sama a yankuna da dama na ƙasashen da Isra’ila ke mamaye da su, ciki har da Birnin al-Quds da Yankin Yammacin Kogin Jordan.
Bisa ga rahoton kafofin watsa labaran Isra’ila, Channel 14 ta kwashe ma'aikatanta, yayin da Channel 12 ta fitar da jama’a daga dakunan shirye-shiryenta bayan jin wannan jiniyar.
Rundunar sojin mamaya ta Isra’ila ta bayyana cewa ta hana wani makami mai linzami daga Yemen shiga sararin samaniyarta, wanda ke zama hari na biyu da aka dakile cikin rana guda.
Amurka Ta Ci Gaba da Hare-hare a Yemen
Bayan harin na Yemen, gidan talabijin na Al-Masirah ya bayyana cewa jiragen saman yaki na Amurka sun kai hare-hare guda hudu kan lardin Hodeidah da ke gabar Tekun Red Sea.
Haka kuma, wata sabuwar luguden bama-bamai ta afkawa lardin Saada da ke arewacin Yemen.
Tun daga ranar Asabar, Amurka ta kai hare-hare da dama, ciki har da wani mummunan hari da ya hallaka mutum 53.
Martanin Hamas da Sake Harin Yemen
Da safiyar ranar Alhamis, Hamas ta bayyana cewa mayakan ta na Al-Qassam sun harba rokoki zuwa Tel Aviv, a matsayin martani ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa fararen hula a Gaza.
Kazalika, Hukumar Tsaron Isra’ila ta ce ta dakile wani makami da aka harba daga Gaza, yayin da wasu biyu suka fado a wuraren da babu mutane.
A safiyar yau, rundunar sojin Isra’ila ta hana wani makami mai linzami daga Yemen shiga kasar, wanda Rundunar Sojin Yemen ta bayyana a matsayin makami mai saurin tafiya fiye da na sauti (hypersonic missile) da aka harba zuwa filin jirgin saman Ben Gurion.
Harin na Yemen ya tilasta kimanin Isra’ilawa miliyan biyu neman mafaka, yayin da hukumar agaji ta gaggawa ta Isra’ila ta tabbatar da cewa mutane 13 sun jikkata sakamakon turmutsutsu yayin kokarin shiga bunkers.
Bayan harin, kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana cewa Firaminista Benjamin Netanyahu ya katse taro a majalisar dokokin Isra’ila (Knesset) sannan ya sauka zuwa mafakar kariya daga hare-hare.
A wani jawabi dabam, Rundunar Sojin Yemen ta bayyana cewa ta sake kai hari kan wani jirgin ruwan yakin Amurka a Tekun Ja, wanda ke zama sabon hari cikin jerin hare-haren da aka kai bayan da Amurka ta kara matsa lamba kan Yemen da hare-haren ta.