Offline

Harin Yemen: An Ji Karar Jiniyoyi A Wuraren Da Israi'la Ke Mamaye Da Su


Isra’ila ta fitar da rahoto cewa an ji karar jiniya a tsakiyar yankunan da take mamaye dasu a Falasdinu, ciki har da biranen Tel Aviv da al-Quds, bayan da ansarullah ta kaddamar da harin makami mai linzami daga Yemen.

Isra’ila ta bayyana cewa an jinkarar jiniyoyin ne da misalain arfe 4:01 na asuba a lokacin da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ke cikin zauren Knesset. Channel 14 ta kasar Isra’ila ta ruwaito cewa Netanyahu an kai shi mafakar garkuwa daga hare-hare yayin da sauran mazauna yankin suka ruga wajen tsira da rayukansu, wanda ya haifar da cunkoso da jikkatar mutane 13 sakamakon harin.

Bayan haka, jiragen sama da ke filin jirgin Ben Gurion an karkatar da su zuwa wasu wurare.

Duk da haka, Isra’ila ta yi ikirarin cewa makamin an tarwatsa shi a sararin samaniyar Saudiyya kafin ya kai ga manufarsa.

Martanin Yemen Kan Sabon Yakin Gaza

Wannan shi ne hari na biyu da rundunar sojojin Yemen (YAF) ta kai tun bayan farfado da hare-haren Isra’ila a Gaza, wanda ke gudana tare da sabbin hare-hare da Amurka ke kai wa Yemen.

A daren Laraba, jiragen yakin Amurka sun kaddamar da sabbin hare-hare kan Yemen, inda suka ragargaza babban birnin Sanaa da yankunan Saada da al-Bayda, kamar yadda wakilin Al Mayadeen ya tabbatar.

A rahoton, an ce hare-haren sun auna wuraren kusa da Ma’aikatar Sadarwa da Hukumar Wasiku a arewacin birnin Sanaa.

A al-Bayda, jiragen Amurka sun kai hari kan gundumar al-Sawadiyah, yayin da a Saada, hare-haren sun shafi yankunan da ke kusa da birnin.

Rahoton SABA, kafar yada labarai ta Yemen, ya bayyana cewa harin Amurka a yankin al-Thawra na arewacin Sanaa ya ritsa da wani ginin biki da ke cikin anguwar jama’a.

A gefe guda, Rundunar Sojojin Yemen (YAF) ta ci gaba da yaki da jiragen ruwa na sojin Amurka, wadanda ke da alhakin hare-haren Yemen, tana kai hare-hare a kan Carrier Strike Group 8 sau da dama.

Post a Comment

Previous Post Next Post