Ƙasa ce da take yankin Gabas ta tsakiya yankin larabawa, tana kusa da teku ne wanda ta ke a yankin Gabas ta tsakiya.
Ta yi iyaka da ƙasashe irin su Jordan,Syria da Lebanon, kuma ƙasar Egypt.
Ƙasar falasɗin; ƙasa ce mai tsawon tarihi da daɗewa wadda ta yaye annabawa da yawa, ma'ana a ƙasar falasɗin suka rayu kuma yanzu haka ƙabarburansu na can.
Ƙasa ce da masallaci mai tsarki ya ke a cikinta, ma'ana masallacin Qudus wanda ya kasance Alqibla ta farko wanda Musulmai ke kallo domin gabatar da Sallah, kafin daga baya a juya zuwa Ka'aba.
Wannan masallaci mai tsarki a yanzu haka Yahudawa ke da iko da shi, suna kokarin ganin sun kashe dukkan Musulmin da ke yankin.
Ƙasar falasɗin tana da yalwan gaske, inda turawa suka fidda ƙasar Israel daga cikin ta domin mamaye ƙasar.
Lebanon da Israel, America ta samar dasu domin mamaye falasɗin su karya ƙadarinta kamar yadda su ke kashe Falasɗinawa a kullum domin cimma manufar su.
Daga shekarar 1948 zuwa yanzu, haramtacciyar kasar ta kashe kashi 10 cikin 100 na Falasɗinawa, wanda ke nuna a kullum haramtacciyar ƙasar Isra'ilan na kashe Falasɗinawa 250 wanda yawancinsu ƙananun yara ne.
Kisan da haramtacciyar ƙasar Isra'ila ke yi bai bar yara da mata ba, hatta a Masallatai,cocina, kasuwanni da asibitoci, da makarantu bomb ake jefa musu tare da rusa gidajensu kusan shekaru 78 kenan zuwa yanzu.
◾Shin haka zamuyi shiru akan al'amarin Falasɗinawa?
-Shin ko munsan wanne hali Falasɗinawa suke ciki a yanzu?
-Shin ko munsan Falasɗinawa su na da haƙƙi a kammu?
-Shin mun san cewa Falasɗinawa suna buƙatar taimakon mu?
Shin munsan kullum kashesu akeyi da rushe gidajensu?
A takaice waɗannan tambayoyin ya kamata mu yiwa kan mu kowa ya tambayi kansa da kansa me kakeyi don neman ƴancin Falasɗinawa?
Lallai ko mun sani ko bamu sani ba Falasɗinawa su na da haƙƙoƙi a kanmu cikin al'ummar musulmi kake ko Kirista.
Wajibin mu ne muyi duk abunda zamu iya don samar wa wannan al'ummar ta Falasdinawa sauki ta hanyar da zamu iya; wa la'alla da kudinmu ne, lokacinmu, da dukkan wani nau'i na taimako da zamu iya.
Muna fatan Allah ya kawo karshen wannan zalunci da haramtacciyar kasar Isra'ila take yiwa al'ummar Falasɗinu nan kusa.
#StopkillingPalestine
#EndOfInjustice
#FreedomForPalestine.
#GazaGenocide
#FreePalestine
Muhammadbaqeer Dahiru Rugoji.
©Freedom Fighters NG.
02/08/2014
Tags
Palestine