Offline

Aƙalla Palasɗinawa 30 Suka Yi Shahada a Harin Da Isra'ila Ta Kai Makarantu Biyu A Gaza.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan 

Masu aikin bada agaji a Gaza sun yi kokarin tono mutane daga baraguzan gine gine a ranar Lahadi da ta gabata sakamakon tagwayen hare hare da Isra'ila ta Kai makarantu biyu wanda suka yi sanadiyyar shahadar aƙalla mutum 30.


Hukumar Civil Defense ta Palasɗinawa ta bayyana cewa harin na ranar Lahadi cigaba ne na harin da Isra'ilar ta kai a ranar Asabar, domin harin irin sa ɗaya da harin na ranar Asabar.


Mai magana da yawan hukumar ta Palestinian Civil Defense Mahmoud Basal, ya bayyana cewa kaso mafi rinjaye na mutanen da aka zaƙulo daga baraguzan gine ginen a ranar Lahadi mata ne da ƙananan yara.


Ya kara da cewa suna tunanin akwai sauran mutane a ƙasan baraguzan gine ginen da ba a kai ga cirowa ba, ya bayyana cewa makarantun sune wurin da mutanen suke rayuwa kafin Isra'ila ta kawo masu wannan harin.


Wani faifan bidiyo ya nuna irin asarar da harin ya haifar na rayuka da dukiya, ta yadda aka ga gawarwaki birjik a filin makarantar bayan harin na Isra'ila, hakanan kuma bidiyoyin sun nuna yadda aka rika daukar yara masu raunuka a Ambulance.


Harin ya lalata sashi uku na makarantar Al-Nasr School daga ɓangaren arewa, hakan wani sashe na makarantar Hassan Salama School, wadannan makarantu biyu sun zama mazaunin daruruwan Palasɗinawa da suka rasa muhalli su, mafi yawancin su mata da ƙananan yara.


Hukumomin Palasɗinawa sun bayyana cewa haramtacciyar ƙasar Isra'ila bata baiwa mazauna makarantun gargaɗi ba kafin harin.


"Da an basu gargaɗi da yawan wadanda suka rasa rayukansu bai kai haka ba" cewar Mahmoud Basal


Wannan hari na ranar Lahadi ya biyo bayan harin da Isra'ila ta kai makarantar Al-Huda da Al-Hamama a ranar Asabar wanda yayi sanadiyyar shahadar mutum 17.


Basal ya bayyana cewa kasancewar harin na farko ya faru kwatsam babu gargaɗi yasa adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya yi yawa, aja cikin kwashe shahidai da masu raunuka ne Isra'ila ta yi gargaɗin cewa wani hari na tafe.

Post a Comment

Previous Post Next Post