Daga - Mahadi Tukur Almizan
Aƙalla gawar mutum 60 aka gano a unguwar Tal Al-Hawa dake maƙotaka da kudancin birnin Gaza yayinda masu bada agaji suke gudanar da bincike masu raunuka bayan sojin haramtacciyar ƙasar Isra'ila sun janye daga unguwar.
Adadi mafi yawa daga cikin gawarwakin mata ne da ƙananan yara, an same su a titunan Tal Al-Hawa bayan sojin Isra'ila sun janye daga unguwar a safiyar ranar juma'a bayan kwashe tsawon mako guda suna ta'addanci a unguwar.
Jami'an Civil defense na Palasɗinawa dake aiki agaji wajen zakulo gawarwakin sun fuskanci takura sakamakon sojin Isra'ila suna kusa da unguwar bayan janyewar tasu.
Shugaban rundunar ta ƴan Civil defense dake Gaza mai suna Mahmoud Basal ya tabbatar ma kafar yaɗa labarai ta Aljazeera cewa sun iya gano gawar mutum 60, yace lamarin babu daɗi sun binne wasu gawarwakin anan wasu kuma sun ɗauke su zuwa asibitocin dake kusa, amma duk da haka akwai gawarwaki dayawa a karkashin baraguzan gine gine, sun kasa ciri su ne saboda barazanar sojin Isra'ila dake kusa da unguwar.
After the complete withdrawal of the occupying forces from Tal al-Hawa and Al-Sin'aa areas, we found dozens of decomposed martyrs' bodies. They destroyed everything; there is nothing left, neither stone nor tree. Tal al-Hawa has become a hill of ashes. pic.twitter.com/eYiKq14pZi
— Eye on Palestine (@EyeonPalestine) July 14, 2024
Basal ya bayyana cewa wasu daga cikin gawarwakin sun fara lalacewa wasu kuma a jikkunan su akwai alamar cewa dabbobi ne suka yi masu rauni wanna yana nuna yadda sojin Isra'ila suka keta alfarmar ɗan Adam.
Kafafen yada labarai na a cikin gida sun tabbatar da cewa mafi yawan waɗanda aka kashe a unguwar ƙananan Yara ne da Mata.
Hakanan a cikin makon nan aka samu gawar wasu Palasɗinawa 60 a Shujaiyya kuma haryanzu akwai adadi mai yawa da ke ƙarƙashin ƙasa gini ya danne su, wannan yayi kama da na Tal Al-Hawa.
Irin wannan munanan labarai suka sa majalisar ɗinkin duniya ƙiyasin cewa haryanzu akwai aƙalla Palasɗinawa 300,000 a arewacin Gaza dake fuskantar barazana da cin zarafin ɗan Adam.
Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa daga fara wannan yaƙi a cikin watan October na shekarar 2023 zuwa yanzu Isra'ila ta kashe Palasɗinawa aƙalla 38,300.

