Offline

Sojin Isra'ila Sun Bi Takan Mahaifiya Da Tankar Yaƙi A Gaban Ɗanta Bayan Sun Harbe Ta.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Tankar yaƙin sojin Isra'ila ta bi takan wata mata a gaban ɗan ta a birnin Gaza a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.


Euro Med Monitor ƙungiya ce ta kare haƙƙin ɗan Adam ta yi bincike kan yadda sojin Isra'ila ke taka Palasɗinawa da Tankar yaƙi a lokuta mabanbanta.


A wani rahoton da Euro Med suka fitar sun bayyana cewa a ranar Alhamis sojin na Isra'ila sun bi takan wata mata mai kimanin shekaru 65 mai suna Safiya Hassan Musa Al-Jamal bayan sun afka gidan ta sun rusa sunji mata rauni.

Wannan lamari ya faru ne a gaban ɗan ta mai suna Muhannad Al-Jamal.


Muhannad ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar ta Alhamis sojin Isra'ila suka shigo gidan su, shi da mahaifiyar su da ƴan uwan shi mata guda 4 sojin sun tattara su a tsakar gida domin su rusa gidan.


Bayan rana tayi sosai sai sojin suka fara harbin bangon gidan da ƙaramin Bom guda 5 domin kada katangun gidan a lokaci guda kuma suna harbi da bindiga, wannan ne yayi sanadiyyar raunata shi da mahaifiyar su.


Hakanan ɗaya daga cikin ƴan uwan Hannad mata mai suna Areeji ta bayyana ma Euro Med cewa wata sojin Isra'ila mace ta faɗi masu ita da Hannad cewa za su kai maman su asibiti.


Haka sojin na Isra'ila suka ɗauki Hannad da maman shi safiya a saman tankar yaƙi zuwa wani Roundabout dake kusa da su sa ake kira 'Mustapha Roundabout anan suka ajiye safiya a ƙasa anan ne suka bi ta kanta da tankar yaƙin a gaban Hannad.


Hannad ya bayyana cewa "Lokacin da naga ana taka mahaifiyata da Tankar yaƙi sainaji kamar na haukace babu abinda nake sai suka" ya kara da cewa hakanan shima ya gudu saboda harbin da sojin ke yi da bindiga.


Rahoton na Euro Med ya nuna yadda sojin na Isra'ila suke taka Palasɗinawa da Tankar yaƙi a lokuta mabanbanta, a cikin watan February ranar 29 ga wata sun taka wata mai mai shekaru 62 mai suna Jamal Hamdi Hassan Ashour a unguwar Zeitoun dake kusa da birnin Gaza.


Hakanan rahoton ya kawo yadda sojin na Isra'ila suka taka iyalin gidan 'Ghannam Family" da tankar yaƙi a Khan Younis a cikin watan January.


Bayan fitar da wannan rahoton kafar yaɗa labarai ta New Arab tayi kokarin jin ta bakin rundunar sojin Isra'ila dangane da lamarin amma basu ce komai ba zuwa haɗa wannan rahoto.

Post a Comment

Previous Post Next Post