Offline

Aƙalla Dalibai 9,241 Isra'ila Ta Shahadantar Daga 07 October Zuwa Yau - Cewar Ma'aikatar Ilimi Ta Palasɗinawa

 


Daga - Abdurrahman Bala Idris

Ma'aikatar ilimin kasar Palestine ta sanarda shahadar akalla dalibai 9,241 da jikkata akalla dalibai 15,182 a zirin gaza da West Bank.


Kamar yadda ma'aikatar ta sanarda cewa a Gaza kadai ansamu shahidai akalla 9,138 da masu raunuka har guda 14,671 tun farkon farmakin Haramtacciyar Kasar Israila kan Palasɗinawa, haka kuma yammacin gabar kogin Jordan wato West Bank ansamu shahidai akalla dalibai 103 da masu raunuka akalla 505 tareda karin dalibai 357 dake tsare agidajen yari.


Hare haren Haramtacciyar Kasar Israila dai sun rushe makarantu akalla 353 inda wasu makarantun aka lalata gine ginensu.


A West Bank kuwa akalla an rusa makarantu 69 ciki harda jami'o'i guda biyar  makarantun gwamnati 133 sun koma sansanin 'yan gudun hijira.


Ma'aikatar ta yi ƙarin haske da cewa dalibai kusan 620,000 basu da halin zuwa makarantun su saboda hare haren da ake fuskanta kuma an dakushe burin masu son shiga makarantun.


Haka kuma ma'aikatar ta yi kira da babbar murya akan a dakatar da hare haren Haramtacciyar Kasar Israilar akan al'ummar Palastinu.



Post a Comment

Previous Post Next Post