Daga - Mahadi Tukur Almizan
Asiri Ya Tonu Ƴan Sandan Turkiyya Sun Kama Jami'an Isra'ila Masu Safarar Sassan Jikin Mutane
Isra'ila ta dade da kasancewa daga cikin manyan masu safarar sassan jikin mutane irin su ƙoda kuma ana zargin suna satar waɗannan sassan jikin ne daga Palasɗinawa da suke kamawa suna kashewa.
A ranar Lahadi 5 ga watan Mayu jami'an ƴan sandan Turkiyya sun kama jami'an Isra'ila guda 5 da wasu ƴan Syria 2 a birnin Adana na kasar ta Turkiyya bisa zargin safarar sassan jikin mutane kamar yadda jaridar SABAH ta wallafa a ranar 5 ga watan na Mayu.
Daraktan hukumar da ke kula da fasa ƙwauri ne ya ƙaddamar da bincike a bakin bodar Isra'ila da Turkiyya ta birnin na Adana tun wata ɗaya da ya gabata an binciki Passport ɗin wasu mutum 7, cikin su akwai mutum 2 ɗan kimanin shekaru 20 da 21 ƴan asalin ƙasar Syria ne an same su da Passport ɗin bogi, sun shigo Turkiyya da sunan yawon buɗe ido.
Da aka ci gaba da bincike angano cewa mutane biyun nan ƴan Syria sun ƙulla yarjejeniya ne tsakanin su da wasu Isra'ilawa kan cewa zasu siyar masu da ƙodar su ɗaya ɗaya, ƴan Isra'ilar masu kimanin shekaru 68 da 28.
Jami'an sun ƙaddamar da bincike a muhallin waɗanda aka kama ɗin kuma an samu zunzurutun kuɗi har dalar Amurka $65,000 da wasu Passports ɗin bogi masu yawa.
Tun a shekarar 2011 ne dai 'Bloomberg' ta bayyana cewa Isra'ila na daga cikin manyan masu safarar sassan jikin mutum a faɗin duniya, inda suke amfani da hatsaniya da faɗa ce faɗa ce da suke faruwa a wasu kasashe masu tasowa suna samun sassan jikin mutane suna siyar ma marasa lafiya dake bukatar a yi masu dashe a kasashen da suka ci gaba.
Binciken Bloomberg ya nuna cewa yanzu safarar sassan jikin mutane ya tashi daga inda aka sanshi a da kasashe irin su Azerbaijan,Belarus, Ukraine Maldova ya koma Isra'ila,Brazil, Philippines, da irin su South Africa.
Zargin safarar sassan jikin mutanen da ake yi ma Isra'ila ya haɗa har da na Palasɗinawa, domin kuwa a shekarar 2009 wata babbar jaridar ƙasar Sweden 'Aftonbladet' ta kawo rahotan shaidar cewa sojojin Isra'ila na garkuwa da Palasɗinawa suna kashe su domin su cire sassan jikin su su siyar.
A rahoton an kawo yadda sojojin Isra'ila suka kama wasu Palasɗinawa a West Bank da zirin Gaza, kuma an dawo ma iyalansu da gawarwakin su babu wasu sassan jikin su.
A cewar wanda ya rubuta rahoton mai suna Donald Bostrom ƴan uwan ɗaya daga cikin su mai Suna Khaled da aka kama a Nablus sun bayyana cewa an ɗauke ƴaƴan su domin a cire wasu sassan jikin su, hakanan Kawun Mahmoud da Nafes da aka kama a Gaza ya bayyana cewa "Duk sun bata ba a sake ganin su ba kawai sai dai aka dawo da gawarwakin su bayan wasu kwanaki an cire wasu sassa na jikin su".
Wannan yaƙin da ya ɓarke tun 07 October ya baiwa Isra'ila damar cigaba da sace sacen sassan jikin Falasɗinawa.
A ranar 30 fa watan January kafar yaɗa labarai ta 'WAFA News Agency' ta kawo rahoton cewa sojojin Isra'ila sun kawo gawarwakin Palasɗinawa 100 da suka sata a asibitoci da maƙabartu a Gaza.
Rahoton likitoci ya nuna cewa andawo da wasu daga cikin gawarwakin babu wasu sassan jikin su.
Wata jaridar Isra'ila ta tabbatar da wannan satar gawarwakin da sojojin Isra'ila suka yi.
A ranar 18 ga watan January jaridar Times If Israel ta kawo rahoton cewa sojojin Isra'ila sun tona wasu ƙaburbura a Maƙabartun Gaza, sai dai sojojin sun bayyana cewa suna bincike ne ko Hamas sun binne mutanen su da suka kama.


