Daga - Mahadi Tukur Almizan
Jami'an sojin Syria sun yi nasarar kashe ƴan ta'addan ISIS a kusa da wani Sansanin Sojin Amurka A Syria.
Kasar Syria da Rasha sun zargi Amurka da horar da ƴan ta'addan ISIS da wasu ƴan ta'addan a sansanin sojin Amurkar dake Al-Tanf.
A ranar 3 ga watan Mayun da muke ciki ƴan ta'addan na ISIS suka ƙaddamar da hare-hare mabanbanta kan dakarun dake goyon bayan sojin ƙasar ta Syria a saharar Al-Sukhna dake yankin Homs ta gabashin kasar ta Syria a cewar kafar yaɗa labarai ta Sputnik's.
Wakilin kafar yaɗa labarai ta Sputnik's a Homs ya bayyana cewa rundunar sojin Syria haɗin gwuiwa da dakarun da ke taimaka mata sun yi nasarar daƙile wannan hari na ƴan ta'addan ISIS inda suka kashe tare da Raunata 40 daga cikin ƴan ta'addan.
A nasu bangaren suma sojin na Syria mutum 13 sun mutu a lokacin da suke musayar wuta da ƴan ta'addan.
Amurka dai na zaune a sansanin na Al-Tanf ne bisa ikirarin yakar ƴan ta'addan na ISIS, sai dai kamar yadda muka kawo Syria da Rasha na zargin Amurka da horar da ƴan ta'addan na ISIS da wasu kamar Syrian Revolutionary Commandos, Ahrar al-shariqiya dakarun Ahmed al-Abdo.
Hakanan kuma duk wani jirgin sojin Syria da ya gitta ta yankin na Al-Tanf sai sojin Amurka sun harboshi.
Ko a ranar 19 ga watan Afrilun da ya gabata aƙalla soji 20 daga rundunar "Liwa al-Quds" ta Palasɗinawa masu taimaka ma Syria ƴan ta'addan na ISIS suka kashe a Al-Sukhna.
Ƴan ta'addan sun hari Bus ɗin su da machine gun da B7 artillery shella yayin da suke tafiya a tsakanin kauyen Al-koum da birnin Al-Sukhna a kudancin saharar Badia kusa da Palmyra.
A ranar Talatar da ta gabata Major General Yuri Popov na Rasha da ke aiki a Syria ɗin ya bayyana cewa rundunar sojin saman Rasha dake Syria sun yi nasarar tarwatsa sansanin ƴan ta'adda biyu bayan sun bar yankin sansanin Amurka na Al- Tanf inda ake zargin suna karbar horo daga sojin Amurka, sansanonin da sojin na Rasha suka tarwatsa maɓoya ce ta ƴan ta'addan a tsaunin Al-Amur dake yankin Homs.


