Sojin Isra'ila sun buɗe ma junan su wuta a bisa kuskure.
Watan Tankar yaƙi ta kuskure ta buɗe ma ƴan uwanta sojin Isra'ila wuta a bisa tunanin ƴan gwagwarmaya ne a sansanin gudun hijira na Jabalia inda ake gwabzawa a halin yanzu tsakanin ƴan gwagwarmaya da sojin na Isra'ila.
Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana ma kafar yaɗa labarai ta 'Times Of Israel' cewa a jiya 15 ga watan May sojojin ta 5 sun riski ajalinsu a Jabalia dake arewacin Gaza sakamakon musayar wuta bisa kuskure.
Sojojin duka daga Paratroopers Brigade's 202 Battalion suke.
Rahoton soji ya nuna cewa Tankar ta harba Shells biyu ne a gidan da ƴan uwan nasu sojojin Isra'ila suke bayan da suka ga bindiga ta ɗaya daga cikin tagogin gidan, amma a cewar su sunyi tunanin ƴan gwagwarmaya ne shiyasa suka buɗe masu wuta.
Ana nan dai ana cigaba da bincike a cewar rundunar tsaron ta Isra'ila.
Ba dai wannan bane karon farko da sojojin na Isra'ila suka buɗe ma ƴan uwan su wuta ba tun daga fara shigowar dakarun na Isra'ila zirin Gaza a watan October na shekarar 2023.
Gwamnatin Isra'ila ta bayyana cewa a Tarihi sojin na Isra'ila sune suka fi kowa kashe ƴan uwan su a bisa kuskure abinda ake kira"Friendly Fire".
Wannan harin na jita Laraba yazo a daidai lokacin da sojin na Isra'ila ke karɓar wuta a hannun ƴan gwagwarmaya a arewacin Gaza musamman ma a Jabalia, duk da iƙirarin da Isra'ila take tayi tsawon lokaci cewa sun gama da ƴan gwagwarmaya.
Rahoto ya bayyana cewa a ƴan kwanakin nan ƴan gwagwarmaya sun canza taku inda suke haɗama sojojin na Isra'ila tarko ta hanyar dasa Bama bamai a cikin gidaje sai su bar gidan idan sojojin Isra'ila suka shiga gidajen sai Bama baman su tashi da su.
Qassam remotely detonates a booby-trapped building vs IDF soldiers in Jabaliya camp. The fighter says, we swear, we will bring you terrible death. Now, advance, to gather your pieces, O cowards. [Qassam Brigades 15/5] pic.twitter.com/pYs4LMTzmF
— Jon Elmer (@jonelmer) May 16, 2024
Ko a makon da ya gabata Tel Aviv ta tabbatar da mutuwar sojinta 5 a Al-Zaytoun sakamakon fashewar bama baman da ƴan gwagwarmayar suka dasa.
A halin yanzu dai a Jabalia ake ta gwabzawa.
Ko a yau 16 ga watan May Qassam Brigades ta fitar da labarin tarwatsa wani gungun sojojin na Isra'ila da makamin Al-Yassin 105 Shella a Block 2 na sansanin Jabalia wanda ya kashe sojin na Isra'ila kuma ya raunata wasu da dama.
Hakanan suma 'Palestinian Islamic Jihad (PIJ) suma sun bayyana irin nasarar da suke samu akan sojin na Isra'ila
Al-Quds Brigades Operations on 15th of May:
— Warfare Analysis (@warfareanalysis) May 16, 2024
TLDR:
- Sniped Israeli sniper: 1
Partially or completely destroyed:
- APCs: 0
- Tanks: 3
- D9 bulldozers: 1
Total Israeli soldiers and officers casualties: at least 13
⚡️Al-Quds Brigades: We inflicted casualties on a Zionist… pic.twitter.com/BXntlVpkcZ


