Daga - Mahadi Tukur Almizan
Shugaban kasar Turkiyya Tayyip Erdogan ya fuskanci matsi daga al'ummar ƙasar bisa cigaba da kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra'ila da ke cigaba da kashe Palasɗinawa a Gaza.
A ranar Alhamis gwamnatin kasar ta Turkiyya ta dakatar da dukkanin wata alaƙar kasuwanci a tsakanin ta da Isra'ila, wannan mataki ƙari ne akan matakin da ƙasar ta ɗauka a watan da ya gabata na takaita kasuwancin wasu ayyanannun abubuwa.
Wadannan matakai duka sun biyo bayan zanga zangar da al'ummar ƙasar suka gudanar kamar yadda kafar Bloomberg ta labarto a juya 3 ga watan Mayu.
Wannan dai wani yunkuri ne na goyon bayan Palasɗinawa, jami'an gwamnatin Turkiyya guda biyu ne suka tabbatar ma Bloomberg wannan matakin na yanke alaƙar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Sai dai Erdogan bai sanar da wannan mataki ba, sannan kuma babu cikakken bayani akan sharuɗɗan da aka gindiya idan Isra'ila na son a gyara alaƙar anan gaba, wanda darajar kasuwancin dake tsakanin su takai kimanin dalar Amurka biliyan biyar ($5billion) kamar yadda 'Turkish Statistical Institute' ta bayyana a shekarar 2023.
Daga fara wannan yaƙi da Isra'ila ta kashe sama da Palasɗinawa dubu 34, Erdogan yake fuskantar matsi daga cikin gida akan cinikayya da Isra'ila ciki har da kayan amfanin soji.
Sai dai labarin yanke alaƙar kasuwancin ya ɓata ma hukumomin Isra'ila rai a matsayin Erdogan na babban abokin su a baya, ciki kuwa har da lokacin da suka taimaka nashi a yaƙar ƴan ta'addan Syria a shekarar 2011, da kuma alaƙar dake tsakanin su ta jigilar mai daga Kurdish region dake arewacin Iraqi zuwa cikin Isra'ila wanda yake biyowa ta tashar jiragen ruwa ta Ceyhan dake Turkiyya tun daga 2014.
Ko kafin ɓarkewar wannan yaƙin Erdogan da Netanyahu suna kan tattaunawa akan yadda buttuutun gas (Gas Pipeline) domin safarar gas zuwa Turai (Europe).
Ministan harkokin wajen Isra'ila yayi Zantuka masu kaushi bisa wannan matakin na Turkiyya a shafin shi na X, sai dai ya bayyana cewa Isra'ila zata yi kokarin maye gurbin wannan alaƙar kasuwancin ta hanyar karfafa masana'antun cikin da kuma hada sabuwar alaka da wasu ƙasashe domin shigo da kaya.


