Daga - Mahadi Tukur Almizan
Rundunar Qassam ta Hamas ta gudanar da mummunan hari kan sojin Isra'ila inda suka kashe tare da raunata sojin na Isra'ila daga karshe kuma suka kama adadi mai yawa.
Ƴan gwagwarmayar ƴanto Palasɗinu na cigaba da gwabzawa da sojojin Isra'ila tsawon kwanaki 232 a jiya Asabar kenan, a cigaba da gwabzawar da ake yi ne dai a jiya asabar adadi mai yawa na sojojin na Isra'ila suka riski ajalin su wasu kuma suka samu raunuka wasu kuma suka shiga hannun ƴan gwagwarmaya.
Wannan ƙwami dai ya faru ne a sansanin ƴan gudun hijira na 'Jabalia Refugee Camp' bayan faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ta Qassam Brigades ya bayyana yadda lamarin ya faru.
A cikin wani sautin murya da rundunar ta Qassam ta saki mai dauke da muryar Abu Obeida , ya bayyana cewa rundunar su ta kashe kuma ta raunata sannan kuma ta kama adadi mai yawa na sojin Isra'ila.
Abu Obeida ya bayyana cewa dafarko dakarun rundunar ta Qassam sun yi ma sojin na Isra'ila shigo-shigo ba zurfi inda suka shiga wani tunnel inda suka yi masu kwanton ɓauna a ciki.
Dakarun na Qassam Brigades sun buɗe masu wuta a daidai inda suka kira 'Point Blank' anan ne suka kashe kuma suka raunata waɗannan.
Bayan nan sai wasu sojojin suka kawo ɗauki inda lamarin ya faru abinda ake kira 'reinforcement' alhali tun kafin zuwan su ƴan gwagwarmaya sun binne abubuwan tashi (Explosive) bayan sun shigo abubuwan suka tashi da su.
Abu Obeida ya tabbatar da cewa sojojin na Isra'ila sun mutu wasu kuma sun samu munanan raunuka sannan kuma sun kama wasu hakanan kuma sun kwashe kayan aikin soji daga gare su (Military Equipment).
Wannan dai shine karon farko da rundunar ta Qassam Brigades ta fitar da sanarwar kama sojojin na Isra'ila tun bayan wadanda ta kama a ranar 07 October 2023.
Bangaren yada labarai na Qassam sun saki wannan faifan bidiyon da ya nuna yadda sojojin na Isra'ila suka mutu ana jansu a kasa a cikin tunnel ɗin sannan kuma zaku iya ganin kayayyakin sojin da aka karbe daga sojojin na Isra'ila.
#بالفيديو | كتائب القسام تستدرج قوة إسرائيلية إلى أحد الأنفاق في #مخيم_جباليا وتشتبك معها من مسافة الصفر وتقتل وتصيب وتأسر جميع أفرادها.#طوفان_الأقصى pic.twitter.com/a5XmPAvN1t
— قناة الميادين (@AlMayadeenNews) May 25, 2024
Wannan hari da ya faru a ranar ta Asabar 25 May ya ƙaryata iƙirarin da Isra'ila take na cewa ta share ƴan gwagwarmaya a sansanin da ma birnin na Jabalia baki ɗaya.
A ƴan kwanakin nan dai Isra'ila na fuskantar kazamen hare hare da bata fuskanta ba tun bayan 07 October, domin ko a ranar Asabar kaɗai ƴan sun tarwatsa tankokin Isra'ila da ake kira Merkava guda 4 ta hanyar amfani da makamin da ake kira al-Yassin RPGs (al-Yassin rocket propelled grenades), hakanan sun harbe wani sniper mai ɗauke da al-Ghoul sniper, sannan kuma sun kashe wani sojan Isra'ila har lahira a al-Qassamiya da ke arewa maso gabashin Sansanin na Jabalia.
Hakanan Al-Quds Brigade sun harba aƙalla mm shells 60 kan wasu sojin na Isra'ila a unguwar al-Qassib dake maƙotaka da Jabalia.


