Offline

ICC Ta Bada Umarnin A Kamo Netanyahu Da Ministan Tsaron Isra'ila, Da Shuwagabannin Hamas Biyu Sinwar, Deif Da Haniyeh.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya 'International Criminal Court' ta bada umarnin kama firaministan Isra'ila da wasu mutum uku bisa aikata laifukan yaƙi a Gaza.


Kotun ta bada umarnin kama Netanyahu da ministan tsaron Isra'ila mai suna Yoav Gallant.


Sai dai abun mamakin shine kotun ta bada Umarnin kama mutum uku daga shugabannin ƙungiyar gwagwarmaya ta Palasɗinawa 'Hamas'.


Shugabannin na Hamas da kotun ta bada umarnin kamawa sune babban kwamandan bangaren soji na Hamas Muhammad Deif, shugaban sashin siyasa ba Hamas Isma'il Haniyeh da kuma shugaban Hamas na Gaza Yahya Sinwar.


Sunayen waɗannan mutane ya fito ne a sanarwar da Ofishin babban Prosecutor na kotun mai suna Karim Khan ya fitar a yau Litinin kamar yadda zakuji a cikin bidiyon dake ƙasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post