Daga - Mahadi Tukur Almizan
David McBride ya gamu da hukuncin ɗaurin shekaru 5 da wata 8 bisa laifin fitar da takardun da ke ɗauke da bayanan kashe kashen da rundunar dakaru na musamman (Special Force) na kasar Australia suka aikata a lokacin yaƙin Afghanistan.
David McBride tsohon lauyan sojoji ne, an zarge shi da satar bayanan sirri na tsaro dake dauke da bayanan yadda sojojin na Australia sukayi wannan ta'addanci da ya saba dokokin yaƙi.
McBride dai ya wallafa takardun ne a kafafen sada zumunta.
A ranar Talata 14 ga watan May kafar yaɗa labarai ta 'The Guardian' ta wallafa rahotan cewa kotun ƙolin babban birnin kasar ta Australia karkashin alƙali Justice David Mossop ta zartar da hukuncin na watanni 27 ga McBride.
Sai dai McBride ya ɗaura aniyar ɗaukaka ƙara inda ya bayyana cewa aikin shi ne bayyana waɗannan bayanai ga al'umma shiyasa ya fitar da takardun.
Dama dai McBride ya saba karbar bayanan sirri daga hannun jami'an tsaro yana fallasawa, domin kusa a tsawon watanni 18 tsakanin 2014 zuwa 2015 ya karɓi bayanan sirri na tsaro a hannun jami'an sojin kasar ya baiwa ƴan jarida a hukumar yaɗa labarai ta Australia (Australian Broadcasting Cooperation) da kuma bayanan sirrin ta'asar sojojin na Australia a Afghanistan.
Takardun dai sun fallasa ta'asar sojin mutanen Afghanistan da basa ɗauke da makami maza da mata yara da manya.
Bayan ya fallasa bayanan jami'an ƴan sandan babban birnin ƙasar sun kai samame ofishin hukumar yaɗa labaran domin tattare duk wasu bayanai dake da alaƙa da bayanan ta'asar sojin.
Bayanan sun bayyana aƙalla yadda sojojin suka kashe mutanen gari marasa makami a lokuta mabanbanta a ƙalla sau 10.
Akwai lokacin da suka kashe wani mutum da ɗan ɗan shi mai kimanin shekaru 6 har cikin gidan su suka same su suka kashe.
Wani rahoto ya nuna cewa hukumomin Afghanistan sun fusata bisa wannan ta'asar ta kashe mutanen da basuji ba basu gani ba, harma hukumomin suka yi barazanar daina aiki da dakarun na Australia.
A nasu bangaren masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam sun yi Allah wadai da wannan hukuncin da aka yi ma McBride inda wani babban lauya a cibiyar "Human Rights Law Center" Kieran Pender ya bayyana wannan rana da aka daure McBride a matsayin wata baƙar rana ga Demokradiyyar ƙasar.


