Offline

A Karon Farko Ƴan Gwagwarmaya Na Bahrain " Saraya Al-ashtar" (Al-ashtar Brigade ) Sun Kai Hari Isra'ila daga Bahrain


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Ƴan gwagwarmaya na Bahrain sun buɗe sabuwar fuskar yaƙar Isra'ila inda suka kai hari a karon farko.

A jiya Alhamis 2 ga watan May ƴan gwagwarmayar na Bahrain mai suna "Saraya Al-ashtar" wadda da turanci ake kira "Al-Ashtar Brigade" suka fitar da sanarwar kai hari Headquarter kamfanin sufurin Isra'ila dake Kudancin birnin Eilat.



" Ƙungiyar ƴan gwagwarmaya ta Bahrain  na sanar da farmakar Hedkwatar sufurin ƙasa ta Isra'ila mai suna "Trucknet" da ke birnin Umm al-Rashrash dake Eilat a ranar Talata 27 ga watan April, ta hanyar amfani da Drone domin nuna goyon baya ga al'ummar Palestinu".

"Ƴan gwagwarmaya na Bahrain muna tabbatar da cewa za mu cigaba farmakar Isra'ila har sai ta daina ta'addancin da take kan al'ummar Palestinu".

A cikin faifan bidiyon da ke kasa zaku iya ganin lokacin da suka tashi Drone ɗin zuwa Isra'ila.


Ƴan gwagwarmaya dake kai ma Isra'ila hari sun kara yawa a gefe guda ga Hezbollah daga Lebanon, Ansarullah daga Yemen , Karamin Hezbollah da wasu bangarorin gwagwarmaya daga Iraqi yanzu kuma ga Saraya Al-ashtar daga Bahrain.


Saraya Al-ashtar (Al-ashtar Brigade) kungiya ce ta ƴan gwagwarmaya ƴan  shi'a masu ɗauke da makamai da ke fafatawa da hukumomin Bahrain tsawon shekaru.



Bahrain dai tana daga cikin kasashen larabawa masu ɗasawa da Isra'ila wadda ta gyara alaƙar ta da Isra'ila a shekarar 2020 ƙarƙashin yarjejeniyar "Abraham Accords".


Hakanan kuma Amurka na da sansani soji a ƙasar ta Bahrain.

©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

Previous Post Next Post