Offline

A Cikin Makon Nan AKa Rantsar Da Putin A Matsayin Shugaban Ƙasar Rasha A Karo Na Biyar.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Vladimir Putin ya zama shugaban kasar Rasha a karo na biyar bayan rantsar da shi da akayi a ranar Talata.

Bikin rantsuwar ya gudana ne a fadar mulkin Rasha da ake kira da 'Kremlin'.

An gudanar da rantsuwar a gaban al'ummar kasar, anyi amfani da kundin tsarin mulkin ƙasar wajen rantsar da shugaba Putin mai shekaru 71 a duniya.

Lauyoyi da alkalai sun hallara a lokacin rantsuwar inda alkalin alkalan kasar Justice Valery Zorkin ya rantsar da Putin ɗin a sabon wa'adin mulkin da zai kwashe shekaru shida nan gaba kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ya tanada.


An rantsar da Putin a matsayin shugaban kasar ta Rasha a shekarar 2000, 2004, 2012, 2018 yanzu kuma gashi a 2024 an sake rantsar dashi wanda ya zama karo na biyar.

Shugaba Putin yaci zaben da ya gudana a ƙasar ne da kaso 87.28% , sai dai ƙungiyar Tarayyar Turai ta soki sakamakon zaben.




Post a Comment

Previous Post Next Post