Offline

Jami'in Sojin Isra'ila Dake Aiki Bangaren Intelligence Ya Baiwa Budurwarsa Ta Facebook Bayanan Sirri Ashe Da Jami'in Sojin Iran Dake Aiki Bangaren Intelligence Yake Soyayya 😃

 


Daga- Mahadi Tukur Almizan

Wata Jaridar Isra'ila mai suna "Israel National New" ta wallafa labarin wani jami'in Intelligence na Isra'ila ya faÉ—a komar jami'in Intelligence na Iran.


Jami'in na Isra'ila dai ya tuttura ma wancan jami'in na Iran bayanan sirri da suka haÉ—a da hotuna da bayanai akan tsarin tsaron sararin samaniyar Isra'ila da suke kira Iron Dome.



Lamarin dai ya faru ne yayinda jami'in na Iran yayi basaja a matsayin mace, inda ya buÉ—e account da sunan mace a sahar Facebook kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta Kan News ta wallafa.


Jami'in na Isra'ila ya tura hotunan harma da Locations É—in da aka girke Iron Dome É—in, yayi hakane a matsayin ya tura ma Masoyiyar shi ta Facebook.


Daga karshe dai hukumomin haramtacciyar kasar sun gano wannan jami'i kuma an yanke mashi hukunci an tura shi zuwa gidan yari.



Mai magana da yawun sojin Isra'ila ya bayyana wa manema labarai cewa " A kokarin da suke na bibiyar abinda sojojin Isra'ila suke aikatawa a kafafen sada zumunta, sun bankado wannan yunkurin na maƙiya wajen karbar bayanai ta hannun jami'an sojin na Isra'ila".


Wannan dai bashi bane karon farko da jami'an sojin Isra'ila ke kwafsawa a kafafen sada zumunta wajen bada bayanan sirri,  a baya bayan nan an samu wani Kwamanda daga cikin sojin na Isra'ila na Unit 8200 da irin wannan aika aikar inda ya tafka kuskuren da ya fallasa Identity É—in sa.

©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

Previous Post Next Post