Offline

WHO Ta Soki Isra'ila Kan Mummunan Harin Sansanin Al-Maghazi, Mutum 70 Su Ka Yi Shahada.




✍️ Mahadi Tukur Almizan.


Babbar hukumar lafiya ta duniya 'World Health Organization' ta yi Allah wadai da mummunan harin Isra'ila kan sansanin ƴan gudun hijira a Gaza da yayi sanadiyyar shahadar Palasɗinawa 70.

Wannan bidiyon da aka wallafa a shafin X wato Twitter ya nuna yadda ake zato mutane daga baraguzan ginin da aka kaima 


WHO ta samu rahotanni masu tada hankali daga ma'aikatan lafiya dake aiki a Gaza na irin matsanancin halin da harin ya jefa mutane shugaban hukumar lafiya na majalisar dinkin duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana haka a ranar Litinin a wani saƙo da ya wallafa a shafin X wato Twitter.


"Akwai yaron da ya rasa gaba ɗaya dangin sa, hakanan shi ma wani Nurse ya rasa nashi dangin, duk an kashe su".


Wannan magana ta Tedros ya biyo bayan kwana ɗaya da wancan mummunan hari na Isra'ila a sansanin al-Maghazi da ke tsakiyar Gaza.


Tedros ya ƙara da cewa "Hukumar lafiya ta Palasɗinawa ta bayyana cewa mutane 70 suka rasa rayukansu, yayin da jami'an lafiya na asibitin Al-Aqsa suka bada rahoton cewa aƙalla mutane 100 suka samu raunuka".


"A halin yanzu dai asibitin na kula da marasa lafiya fiye da yadda ma'aikatan su zasu iya baiwa kulawa".


" Dayawa ba zasu tsira ba" Tedros yayi gargaɗi kuma ya ƙarfafa cewa wannan mummunan harin ya ƙara nuna dalilin da yasa muke buƙatar a tsagaita wuta a Gaza.

A wannan bidiyon kuma an nuna ya irin barnar da wannan harin yayi ka rushe rushe


Tedros ya bayyana cewa WHO tayi matuƙar damuwa kan irin matsanancin halin da ake ciki a asibitoci a faɗin Gaza da suka rage ana aiki, wanda su kansu da suka rage sun kusa durƙushewa.



©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

Previous Post Next Post