✍️ Mahadi Tukur Almizan
Dakarun haramtacciyar ƙasar Isra'ila na cigaba da ta'addanci a Gaza a mako na 12, a tsawon wannan lokaci sun kai hare hare babu adadi ta sama wanda ke sanadiyyar mutuwar fararen hula.
Hakanan kuma tankokin yaƙin na Isra'ila sun kutsa wasu unguwanni a tsakiyar birnin na Gaza wanda su ma sun kashe fararen hula da dama.
A shekaran jiya juma'a zuwa safiyar asabar hare haren sun tsananta a al-Bureij, Nuseirat da Khan Younis a lokaci guda kuma suna luguden wuta ta sama wanda ya cika asibitoci da masu raunuka.
A cikin awanni 24 da suka gabata sun kashe aƙalla Palasɗinawa 100 inda wasu 150 suka samu raunuka kamar yadda wani babban jami'in lafiya daga Gaza suka bayyana.
An kai mutane da yawa asibitin Nasser dake Khan Younis wanda shine babbar cibiyar lafiya a yankin kamar yadda wasu hotuna da Red Crescent ta wallafa.
Aƙalla mutanen Gaza miliyan 2.3 wannan ta'addanci na Isra'ila ya raba da gidajen su cikin waɗannan satuttuka 12.
Isra'ila ta ƙaddamar da waɗannan hare hare na ta'addanci ne a ranar 7 ga watan Oktoba tun bayan da ƴan gwagwarmaya suka kai wani harin bazata wanda aka yi ma laƙabi da "Ɗufaanul AQsa".
©️ Freedom Fighters Ng
Wannan ta'addancin na Isra'ila ya yi sanadiyyar rasa rayukan aƙalla Falasɗinawa dubu 21, mafi yawancin su mata da yara ne, wasu kuma dubu 55 sun samu raunuka.
Harin Bama Baman Isra'ila ya laƙume gidaje, shaguna da wuraren kasuwanci.
