Shugaban wani kwamiti da ake kira "Israeli Government Oversight Committee, mai suna Mickey Levy yayi gargaɗin cewa haramtacciyar ƙasar sa ta Isra'ila na fuskantar matsin tattalin arziki mai muni a ƙarƙashin mulkin firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu.
Mickey Levy yayi waɗannan kalamai ne a lokacin da yake zantawa da kafar yaɗa labarai ta Yahudawa mai suna "Maariv" inda ya bayyana cewa an tafka maguɗi a cikin kasafin kuɗin kasar domin ayi wasoso.
Mickey ya bayyana cewa an yi aringizon wasu abubuwa a cikin kasafin kuɗin na shekarar 2023, inda aka zuba shekels miliyan 600 domin yaɗa al'adun Yahudanci, ya ƙara tambayar cewa anya kuwa akwai buƙatar kashe maƙudan kuɗaɗe irin waɗannan akan hakan?
Ya ƙara da cewa akwai ma'aikatu marasa amfani a cikin gwamnatin ta Benjamin Netanyahu, yace da can akwai ma'aikatu (Ministries) kasa da 30, amma yanzu akwai ma'aikatu 38, wanda a cewar aƙalla guda 10 ba a da buƙatar su.
Ya ƙara da cewa yanzu ana wani lokacin da kowane shekel ( kuɗin kasar kamar ace Naira) yana tafiya wajen yaƙi amma babu wanda ya damu da hakan.
A ƙarshe ya bayyana cewa a wannan sabuwar shekarar da za a shiga ta 2024 kasafin kuɗin zaifi na baya ta'azzara, yace a ƙarnuka masu zuwa za a cigaba da fama da matsalar bashi wadda ba za a iya kauce mata ba.

