Offline

Firaministan Afghanistan Zaije Iran Taro Kan Al'amarin Palasɗinawa.

 


✍️ Mahadi Tukur Almizan

Tehran zata karɓi baƙuncin wakilan kasashen duniya a taron goyon bayan Palasɗinawa da zai gudana a kasar Iran.


Ma'aikatar harkokin wajen Afghanistan ta tabbatar da Amir Khan Muttaqi, wanda yake jagorantar ma'aikatar harkokin wajen kasar zai kawo ziyara Iran domin halartar taron da za ayi kan yaƙin dake gudana a Gaza.


Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ce ta shirya wannan taro domin tattauna kan al'amarin Palasɗinawa da ƙasar su da kuma al'amarin tsaron ƙasashen waje, taron zai samu halartar jami'an gwamnatocin kasashen duniya.



Idan bamu manta ba dai a cikin watan Nuwamba da ya gabata Ofishin Ma'aikatar harkokin ƙasashen waje na ƙasar ta Afghanistan ya fitar da takardar manema labarai inda ya yi kira ga majalisar ɗinkin duniya ta gaggauta kawo ƙarshen ta'addancin Isra'ila a Gaza.


Hakanan kuma acikin watan na Nuwamba Afghanistan ta tura tawagar masana tattalin arziki zuwa Iran domin bunkasa harkokin kasuwanci, sufuri, harkokin more rayuwa da kuma cigaban ƙasa ciki kuwa har da lamarin yawaitar ƴan gudun hijirar Afghanistan a Iran.

©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

Previous Post Next Post