Offline

Tun Da Aka Ƙaddamar Da Operation Ɗin Al-Aqsa Flood Shugaban Rundunar IRGC Ya Tare A Lebanon.

 


✍️ Mahadi Tukur Almizan | Freedom Fighters Ng


Shugaban rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Esma'il Qaani ya tare a Lebanon domin gudanar da ayyuka a rundunar Hizbullah wajen fuskantar Isra'ila.


Wata majiya ta bayyana ma jaridar Amwaj cewa Kwamandan na rundunar IRGC yana kasar Lebanon kuma yana aiki tare da rundunar Hizbullah.


Majiyar ta bayyana cewa Qaani ya sauka Lebanon ne kwana ɗaya da ƙaddamar da Operation Al-Aqsa Flood da aka ƙaddamar a ranar 7 ga watan Oktoban da ya ƙare, wato Qaani ya sauka Lebanon ranar 8 ga watan Oktoba.


Majiyar ta bayyana cewa Qaani ya bar Lebanon, ya tafi meeting a tsakanin 16 zuwa 20 ga watan Oktoba, tun bayan nan kuma Qaani ya kasance a Lebanon domin yin aikin da ya kawo shi na taimakawa wajen fuskantar Isra'ila a gumurzun dake gudana a  kudancin Lebanon da Isra'ila.



Bayan dawowar Qaani Lebanon ya gana da shugabannin ƙungiyar Hizbullah da na ɓangarorin gwagwarmaya na Palasɗinawa, anyi wannan tattaunawa ne domin isar da saƙon jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Sayyid Qa'ed ga bangarorin dake yaƙar Isra'ila.


Jaridar ta Amwaj ta bayyana cewa Sayyid Hasan Nasrullah shi ne jagoran wannan Operation.


Dogaro da bayanan da ɗaya daga cikin ƴan majalisar dokokin ƙasar ta Lebanon  Hassan Fadlallah yayi a lokacin da yake zantawa da jaridar Al-Mayadeen.


" Babban sakataren ƙungiyar Hizbullahi yana kula tare da sa'ido akan abinda ke faruwa a kudancin Lebanon".


"Sayyid Nasrullah ya na bibiyar dakarun dake wannan yaƙi awa bayan bayan awa, shi ke kula da dukkanin abinda ke gudana, yana da sadarwa kaitsaye da kwamandojin dake bakin daga", a cewar Hassan Fadlallah a ranar 22 ga watan Oktoba a lokacin da yake zantawa da jaridar Al-Mayadeen.


Tun bayan wannan Operation na Al-Aqsa Flood Hizbullah ta ƙaddamar da yaƙi akan matsugunan sojojin haramtacciyar ƙasar Isra'ila dake kudancin Lebanon, zuwa yanzu dai Hizbullah ta kashe sojojin Isra'ila da dama kuma akwai masu raunuka, sannan kuma sunyi nasarar lalata aƙalla tankokin yaƙin Isra'ila da ake kira "Merkava", hakanan ita ma Hizbullah ta samu shahidai, wanda Sayyid Nasrullah ya bada umarnin a kira su da "Shahidan Quds"


Sayyid Nasrullah zai gabatar da jawabi a karon farko tun bayan wannan Operation a ranar juma'a mai zuwa 3 ga watan Nuwamba da muka shiga.


✍️ Mahadi Tukur Almizan | Freedom Fighters Ng

👉🏼https://chat.whatsapp.com/LW41Y9UlF583rVvs0gVEDg

Post a Comment

Previous Post Next Post