Offline

SHEIKH ZAKZAKY (H) YA MIKA SAKON TA'AZIYYA GA AL'UMMAR DA ABALIYAN RUWA YA RUTSA DASU A LIBYA.

 


Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), ya Mika ta'aziyya ga al'ummar Libya da ma É—aukacin al'ummar Musulmi dangane da mummunan bala'in ambaliyar ruwa da ya auku a gaÉ“ar Bahar Rum na wannan Æ™asar. Wanda kuma ya yi sanadin hasarar rayukan  dubban 'yan'uwanmu tare da haddasa É“arna mai tarin yawa.


Duk a cikin sakon yake cewa "Abin baƙin ciki ne ganin wannan ya auku ne ƙasa da mako guda da yin girgizar ƙasa a Maghrib (Maroko) wanda ya yi sanadiyar rasa rayukan sama da mutane dubu uku.


Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan ambaliya, Ya kuma baiwa iyalansu haƙuri da juriya. Allah Ya gaggauta kawo sauƙi ga waɗanda suka sami raunuka.


Muna roƙon Allah Ta'ala da ya kiyaye aukuwar irin waɗannan musibu a duniyar Musulmi".


Sakon jajen yazo ne ta shafin shehin malamin na sada zumunta watohm  SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY OFFICE .


® Imamu Mahadi Umar kaita

    FFNG Hausa.

Post a Comment

Previous Post Next Post