Sojojin Isra'ila sun harbe wani Bafalasdine har lahira tare da jikkata wasu akalla hudu - biyu na cikin mawuyacin hali - a garin Nablus da ke yammacin gabar kogin Jordan, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasdinu da kuma kungiyar agaji ta Red Crescent suka sanar.
Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce an harbe wani mutum kafin wayewar safiyar Alhamis, yayin da mayakan Falasdinawa suka ce suna tunkarar sojojin Isra'ila da mazauna yankin Nablus , kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce akalla Falasdinawa hudu ne suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga, biyu kuma na cikin mawuyacin hali, a wani abin da ta bayyana da arangama da sojojin Isra'ila a gabashin Nablus, wani birni da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan wanda ya kasance cibiyar al'adar gwagwarmayar Falasdinawa ga mahukuntan ƙasar Isra'ila.
Bataliyar Nablus ta dakarun al-Quds Brigades, reshen kungiyar Islamic Jihad da ke dauke da makamai, ta ce membobin ta na yakar sojojin mamaya da kungiyoyin mazaunan da ke kai farmaki a yankin kabarin Annabi Yusuf, tana mai nuni da wurin a matsayin wani wurin ibada a birnin da ke da yawan waƙi'oi tsakanin Falasdinawa da sojojin Isra'ila.
Sojojin Isra'ila ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba game da kisan na baya-bayan nan da aka yi wa Bafalasdinen, wanda ya biyo bayan farmakin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a farkon wannan wata a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin - wanda ke da nisan kilomita 41 daga nesa - wanda ya kashe Falasdinawa 12 tare da jikkata kusan wasu 100, sun sa dubbai tserewa, kuma sun yi barna mai yawa a kan ababen more rayuwa na farar hula.
A watan Fabrairu, sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa 11 tare da raunata fiye da mutane 80 - wasu daga cikinsu raunukan su sun yi muni - a wani samame da suka kai Nablus da ya hada da sojoji 150 da motoci masu sulke da dama. Wannan farmakin ya biyo baya nekasa da wata guda da kashe Falasdinawa 10 a wani hari makamancin haka a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.
.jpeg)