Offline

Jiragen Yaƙin Isra'ila Sun Kai Hari Birnin Syria, Sojojin Syria Biyu Sun Mutu.

 


- Freedom Fighters Ng
Da safiyar yau laraba 19 ga watan Yuli jiragen yaƙi mallakin ƙasar Isra'ila sun kai hari ta sama babban birnin ƙasar ta Syria Damascus.

Wannan hari na yau shine hari na ashirin (20) da Isra'ila takai ƙasar ta Syria a wannan shekarar.

Sojojin ƙasar Syria biyu sun gamu da ajalinsu a sakamakon wannan hari, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta SANA ta ruwaito.

Da misalin ƙarfe 12:25 na dare Isra'ila ta aika jiragen ta ɗauke da makamai masu fashewa daga yankin Golan, inda ta auna wasu muhimman wurare a gefen birnin Damascus a cewar wani jami'in tsaro yayin da yake zantawa da  SANA.

Sai dai jami'an tsaron ƙasar sunyi nasarar kakkabe wasu daga cikin makaman da jiragen ke ɗauke dasu ta hanyar amfani da tsarin  kariyar sararin samaniya na ƙasar.

Banda asarar rayukan sojojin biyu majiyoyin cikin gidan sun bayyana cewa an samu asarar dukiya a wuraren da harin ya auku.

Wata hukumar kare haƙƙin ɗan adam (Syrian Observatory for Human Right) ta ce harin na yau an auna wasu muhallan sojoji ne da kuma wani gidan ajiya mallakin Hizbullah ta ƙasar Lebanon wadda ke ƙawance da ƙasar ta Syria.

A mako biyu da suka gabata ma Isra'ila ta kai hari makamancin wannan a kusa da Birnin Homs, wanda ya haddasa asarar dukiya batare da ansamu asarar rai ko jikkata ba.

Tun daga shekarar 2011 da  Amurka ta fara yaƙi da Syria  ne dai Isra'ila ke kai hare-hare ƙasar ta Syria.

Post a Comment

Previous Post Next Post