Offline

Anyi Garkuwa Da Jami'ar Tsaron Isra'ila Elizabeth Tsurkov A Iraƙi, Palasɗinawa Sun Nemi Asaki Fursunonin Su 5000 A Musayarta.

 


- Freedom Fighters Ng

Anyi garkuwa da wata mai bincike kuma tsohuwar Jami'ar tsaron Isra'ila Elizabeth Tsurkov a ƙasar Iraqi tun a watan march, an zargi ƙungiyar ƴan gwagwarmaya ta Kata'ib Hizbullah da alhakin garkuwa da ita.


Sai dai kuma ƙungiyar fursunonin Palasɗinawa ta yi kira ga Iraqi da suyi yarjejeniya da Isra'ila akan a saki fursunonin su dubu biyar (5,000) da Isra'ilar ke tsare dasu.


Kwamitin fursunonin Palasɗinawa da na rundunonin ƴan gwagwarmaya sun shirya gangami a gaban hedkwatar hukumar lafiya ta RED CROSS da ke Gaza.


A tawagar masu gangamin akwai tsofaffin fursunoni da suka samu ƴanci da malaman addini da wakilan bangarorin siyasa na Palasɗinawa, kamar yadda jaridar Al-Quds ta ruwaito.


 Elizabeth Tsurkov ƴar shekara 36 a duniya mai sharhi ce a yankin na gabas ta tsakiya sannan kuma tsohuwar Jami'ar soji ce a bangaren (Intelligence Department).


An bayyana cewa a lokacin da aka ɗauke ta, an ɗauke ta ne ta hanyar amfani da mata sanye da kakin jami'an tsaron ƙasar Iraqi, kamar yadda majiyoyi suka bayyana ma jaridar The Cradle.


Bayan awa 5 da sakin labarin da The Cradle tayi sai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fito yana zargin ƙungiyar ƴan Shi'a ƴan gwagwarmaya mai suna Kata'ib Hizbullah da aikata wannan ƙwamushe na tsohuwar Jami'ar su.


Ƙungiyar Kata'ib Hizbullah dai na daga cikin ƙungiyoyin maƴaƙa da aka ƙirƙira a ƙasar Iraqi domin fattakar ƙungiyar ƴan ta'adda ta ISIS a shekarar 2014.

Post a Comment

Previous Post Next Post