Offline

Al'ummar Musulmi Bazasu Yarda Da Cin Mutuncin Qur'ani Ba - Cewar Shugaban Kasar Iran

 


- Freedom Fighters Ng

Shugaban Kasar Iran Ibrahim Raisi ya bayyana cewa al'ummar musulmi ba zasu lamunci cin mutuncin Qur'ani mai tsarki ba daga kasashen yamma.


Shugaban na Iran ya bayyana haka ne a lokacin Sallar juma'a a birnin Rafsanjan dake yankin Kerman, yayinda yake magana akan aika aikar kona Qur'ani mai tsarki da a babban birnin kasar Sweden a lokacin wata zanga zanga da jami'an tsaron kasar suka baiwa kariya a  daidai lokacin da al'ummar musulmi ke gabatar da bukukuwan babbar sallah a fadin duniya.


Raisi ya kara da cewa an nuna rashin girmamawa ga saukakken littafi mafi daraja a daya daga kasashen yamma masu ikirarin kare 'yancin tofa albarkacin baki.


Ya kara da cewa ba kawai iya al'ummar musulmi mutum biliyon biyu aka fusata ba, harda sauran mabiya saukakkun addinai (Ahalul-kitabi).


"Domin cin mutuncin Qur'ani, cin mutunci ne ga dukkanin saukakkun litattafai da kuma 'yan adamtaka kuma lallai al'ummar musulmi bazasu lamunci hakan ba"

Post a Comment

Previous Post Next Post