Da asubahin ranar Alhamis ne sojojin Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila suka ruguje gidan wani Bafalasɗine da suke tsare dashi, gidan Bafalasɗinen dai yana a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Gungun sojojin Haramtacciyar Ƙasar ta Isra'ila da yawa ne suka kai farmaki tsohon birnin Ramallah, inda suka rusa gidan iyalan Islam Farouk mai shekaru 27.
Shaidun gani da ido dai sun bayyana ma manema labarai cewa dakarun sojojin na Isra'ila sun shafe tsawon lokaci suna dasa abubuwa fashewa a gidan kafin ginin ya zube.
Wani faifan bidiyo da aka ɗauka ya nuna yadda sojojin suke dasa abubuwan fashewar a jikin katangar gidan kafin daga bisani wani babban abun fashewa ya tarwatsa gidan.
Mahafiyar Islam Farouk ta bayyana cewa har yanzu ana tsare da ɗanta batare da shari'a ba, yanzu kuma anzo masu da wannan zaluncin.
