Wani bafalasdine tsohon fursunan gidan yarin haramtacciyar kasar Isra'ila ya gamu da ajalinsa a wani kwanton bauna da sojin HKI suka yi a Jenin.
Ashraf Muhammad Ibrahim mai shekaru 37 wanda ma'aikacin General Intelligence Service ne a falastin, ya samu raunuka sanadiyyar farmakin da sojin HKI din suka kai a Jenin wanda yayi sanadiyar mutuwarsa kamar yanda ma'aikatar lafiyar kasar ta sanar tareda raunata akalla falasdinawa takwas da kuma kama falasdinawa shida.
Shahadar Ibrahim shine ya kara adadin mutanen da sojin HKI din suka kashe a kwanakin nan da suka kai 56.
Sojin HKI dai kusan kowace rana suna kai irin wadannan farmakin a garuruwa mabanbanta, inda suke ikirarin suna neman falasdinawa ne da ake nema ruwa a jallo wannan yunkurin nasu yana haifarda hatsaniya duk sanda suka kawo farmakin.
A watannin baya Israila ta zafafa hare harenta ga alummar garuruwa da kauyukan falasdinawa aduk fadin guraren da suka mamaye wanda yayi silar mutuwar da yawa hadi da kamawa da kuma raunata falasdinawa.
Nablus da Jenin sune manyan guraren da sojin HKI din suka fi farmaka don dakile tasowar kungiyoyin gwagwarmayar falasdinawa a garuruwan da Israilar ta mamaye.
Sabon farmakin da suka kai dai shine wanda suka kai a masallacin Qudus, wanda ya janyo Allah wadai ga HKI daga sassan duniya.
