Sojojin ruwan Iran sun gano wani jirgin sama da sojojin ruwan Amurka ke yin leken asiri dashi a tekun Oman tare da tilasta masa kaucewa sararin samaniyar kasar bayan sun yi gargadi, in ji rundunar sojin ruwan.
Ma'aikatar hulda da jama'a ta rundunar sojojin ruwa ta Iran ta fada a yammacin jiya Lahadi cewa wani jirgin sama samfurin EP-3E na sojojin ruwan Amurka na shirin kutsawa cikin sararin samaniyar kasar Iran a kan tekun Oman.
Sanarwar ta kara da cewa, dakarun sojin ruwa na kasar Iran masu taka-tsan-tsan sun baiwa jirgin gargadi tare da hana shi shiga sararin samaniyar Iran ba tare da izini ba.
Rahotanni sun ce jirgin na Amurka ya yi kunnen uwar shegu da gargadin, inda ya nisanta daga kan iyakar Iran tare da komawa hanyoyin da kasashen duniya ke bi.
Lockheed EP-3 shine nau'in binciken siginar lantarki na P-3 Orion, wanda Sojojin ruwan Amurka ke sarrafawa.
A watan Oktoban shekarar 2022, mataimakin ministan tsaron kasar Iran ya bayyana irin gagarumin ci gaban da kasar ta samu a masana'antar tsaron sararin samaniya, yana mai cewa sojojin kasar sun tare wani jirgin leken asiri na makiya a nesa mai nisan kilomita 400.
- Mahadi Tukur Almizan
