Wani Bafalasdine ya yi shahada sakamakon harbin sojojin mamaya na ‘Isra’ila’, a masallacin al-Aqsa da ke birnin Quds da aka mamaye a ranar Juma’a.
Kafofin yada labaran cikin gida sun ce an harbe matashin ne bayan ya yin artabu da sojojin yahudawan sahyoniya da ke kofar Silsela [Bab al-Silsela] a lokacin da suka far wa wata Bafalasdiniya da ke yunkurin shiga masallacin, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana.
Shaidun gani da ido sun ce cikin kasa da minti daya ne aka ji karar harbe-harbe guda 20, wanda ya yi sanadiyyar raunata wani mutum guda.
Dakarun mamaya na yahudawan sahyoniya sun rufe kofofin masallacin bayan dubun dubatar masu ibada sun bar harabar masallacin bayan sallar isha'i na watan Ramadan. 'Yan sanda sun hana kowa komawa don ci gaba da sallar dare, kamar yadda kafafen yada labaran Falasdinu suka ruwaito.
Hotunan da aka yada ta yanar gizo sun nuna wani mutum yana kwance a kasa kusa da kofar Silsela da jami'an 'Isra'ila' a tsaye a kusa.
Daga baya an bayyana shahidin a matsayin Mohammad al-Asaibi [26], mazaunin garin Huwwara a yankin Naqab da aka mamaye.
Wani shaidan gani da ido da ya rage tare da wasu tsirarun masu ibada a cikin masallacin al-Aqsa ya shaidawa kafar yada labaran kasar ta Al Jarmaq News cewa, sun ji karar harbe-harbe, ya kara da cewa dakarun ‘Isra’ila’ sun shiga harabar masallacin domin cire tutocin da masu ibada suka kafa da safiyar yau. bayan sallar Juma'a.
Jama'a sun yi ta rera taken bayan kammala sallar tare da sanya alamun nuna goyon baya ga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu.
Masallacin ya cika makil da Falasdinawa kusan 250,000 wadanda suka yi tururuwa zuwa wurin domin yin sallar Juma'a ta biyu a watan Ramadan, kamar yadda alkalumman da mahukuntan masallacin suka bayar suka nuna.
