Gidauniyar Zahra Relief Foundation ta ci gaba da gabatar da rabon abincin buda-bakin azumin Ramadan kamar yadda ta saba a shekarun baya, inda ta raba abincin a muhallan al'ummar musulmi a unguwanni daban-daban.
A jiya Litinin 10 ga watan Afrilu, 2023, an yi rabon ne a s hiyar Area 1 da ke babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja. Mutane da dama ne suka anfana.
Zahra Relief Foundation gidauniya ce a Harkar Musulunci, karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky(H), da ke bayar da tallafi ga marayu, gajiyayyu da sauran mabukatan al'umma bakidaya.
Ramadan kareem
©Freedom Fighters NG
11th April, 2023