Offline

Dakarun Isra'ila sun kashe wani yaro Bafalasdine a farmakin da suka kai Jericho

Bafalasdine Mohamed Faiz Balhan mai shekaru 15

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun harbe wani yaro Bafalasdine har lahira a wani samame da sojoji suka yi a birnin Jericho da ke yammacin gabar kogin Jordan a ranar Litinin.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da cewa an harbe Mohamed Faiz Balhan dan shekaru 15 a safiyar yau sakamakon harbin da Sojojin suka masa a kai, kirji da ciki bayan kai farmaki sansanin 'yan gudun hijira na Aqbat Jabr da ke kusa da Jericho domin kame Falasdinawa.


Ma’aikatar lafiya ta kasar ta kara da cewa akalla wasu mutane uku sun samu raunuka, biyu kuma dauke da harsashi mai rai.

Tun daga farkon shekarar 2023, sojojin mamaya na Isra'ila sun harbe Falasdinawa 98 har lahira, ciki har da yara 18 da wata tsohuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post