بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وآل محمد
إسم: عبدمناف (ع) عم النبي (ص) ، الأب: عبدالمطلب بن هاشم، الكنية: أبوطالب، الزوجته: فاطمة بنت اسد أم الإمام علي (ع) ،الأولاده: طالب/عقيل/جعفر/علي/جمانة/فاخته/أم هاني و اسمها
Abudalib (as) ya kasance dattijo kwarai da gaske dan yana cikin dattawan makkah, sannan ya bada gudummuwa mai girman gaske a musulunci har yakai cewa (Manzon Allah (s) yace badan kariya ta Abudalib da dukiyar Khadija da takobin Aliyu (as) da wannan addinin bai tsaya da kafafun saba)
Abudalib ya kasance yana matukar son Manzon Allah (s) so na kauna
Lokacin da aka aiko Annabi Muhammad (s) zuwaga mutanensa makusan tansa, Abudalib ya gasgatashi kuma yayi amanna da abinda yazo dashi daga gun Allah madau kakin sarki.
Sai dai bai-baiyana imaninsa ba gaba dayaba, ya buye imaninsa daya tsayu da taimakawa Annabi da sauran magoya bayansa.
Abudalib bai taba bautar gumakaba, ya kasance yana bautar Allah da kadai tashi a addinin da Annabi Ibrahim (as) yazo dashi.
Manzon Allah (s) ya damu sosai a lokacin da yaji rasuwar amminsa Abudalib (as) an ruwaito daga Manzon Allah (s) yana cewa:-
ياعم ربيت صغيراً، وكفلت يتيماً، ونصرت كبيراً، فجزاك الله عني خيراً
Ya ammi ka rai neni lokacin da ina karami, ka kuladani lokacin da ina maraya, ka kuma taimakan lokacin dana girma, Allah ya saka maka da mafi alkairi.
Haka kuma Manzon Allah (s) ya jadda da muwarsa yana mai cewa:- Hakika musibu biyu sun sami wannan al'umma, bansan wacce tafi damuna ba,
Haka nan kuma yazo cewa lokacin da (Quraishawa) suka tsananta cutarwarsu ga manzon Allah (s) yace:-
مانالت مني قريش شيئاً أكرهه حتى مات أبو طالب
Hakika basu cutar dani komaiba har saida Abudalib (as) yayi wafati.
Hakika wannan shekara tazama shekarar bakin ciki, cikin tane Sayyida Khadija (s.a) tai wafati tsakaninta da Sayyidina Abudalib (as) kwana uku ne shi yayi wafati 7 gawatan ramadan ita kuma 10 gawatan saboda hakane manzon Allah (s) yakira wannan shekara, shekarar bakin ciki عام الحزن
Hakika Manzo Allah (s) yanajin radadin abinda (Qurai-shawa) suka sasu aciki, sai Abudalib ya kira Manzon Allah (s) sai Manzo Allah yazo, Abudalib yana cewa yakai dan dan uwana yace katafi kayi abinda kake so na rantse da Allah bazan taba sallama maka har abada, Hakan Abudalib (as) ya tsayu mai taimakon Manzon Allah (s) wajen isar da sakon musulunci.
Hakika Abudalib ya kasance yana kula da Manzon Allah kuma ya tarbiyantar dashi ya taimakeshi kuma yana kareshi ta duk inda quraishu suka biyo Abudalib (as) zai kare Manzo Allah (s) bai bari wani abu ya cutar da Manzon Allah ba har yazu wafatinshi.
Abudalin ya kasance mutum ne mai kyautatawa ga Addini, ya kasance tsayayye, rayuwarsa ta kasance mai hidimtawa dansa Manzo Allah (s) har bayan ba ransa Manzon Allah yayi rashin babban uba kuma yayi kuka sosai bayan rasuwarsa, yaji radadin da bai taba jiba har bayan wafatinsa.
AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GAREKA YA AMMIN ANNABIN RAHMA (S)
وصلى الله على محمد وآل محمد
©FREEDOM FIGHTERS NG
.jpeg)