Offline

Wanene Imam Muhammad Al-baqeer ?




 Muna taya ɗaukacin Al-ummar musulmi murnar da kewayowar haihuwar Jikan Manzon Allah (S) wato Imam Muhammad Al-Baqiru Al'ulum (S) ɗaya daga cikin Limaman shiriya.


Muhammad bin Ali (AS) wanda aka fi sani da Al-Baqir ma'ana (wanda ya buɗe ilimi) shi ne limami na biyar daga cikin limaman shi'a, Shi ne ɗan Ali bin Hussain (AS) Wanda akafi sani da Zainu Al-Abidin (AS) kuma Imam na farko wanda ya fito daga jikokin Muhammad da Hasan bin Ali da Hussaini bin Ali tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata a gare su.


 Musulmai Sunni da Shia suna matuƙar girmama shi saboda shugabancinsa, iliminsa da kuma ilimin addinin Musulunci a matsayin masanin shari'a a Madina, shine wanda tun kafin a haife shi da kusan tsawon zamani Annabi (S) ya bada saƙo ga wani Sahabin sa Mai girma mai suna Jabir bin Abdullahi Al-Ansari (RA) Annabi yace; in an haife shi ya miƙa masa saƙon gaishwar sa gare shi, yace Annabi kakan sa yana gaishe shi.


 Bayan wafatin Ali bin Hussain (AS) (Imami na huɗu), mafi yawan ƴan Shi’ar sun yarda da ɗansa Al-Baqir a matsayin Imami na gaba; amma an samu wasu kuma daga cikin ba biya Ahlilbaitin suka ce; wani ɗan Imam Alin ne Imami Wanda ake kiran sa Zayd bin Ali shi ne imami na gaba, shi yasa ya zama ake kiran wasu ƴan shi'ar Zaidiyyah. 


RAYUWAR SA: 

Haihuwa Madinah ranar Jumma'a a cikin watan Rajab an saɓunta kwanakin a shekara ta 57 Hijiriyyah, 8 Mayu 676 Miladiyah.


SARAKUNAN ZAMANIN SA: Umayyad Caliphate.


DANGIN SA:

Mahaifi Ali Ibn Hussain (AS)

Mahaifiyar sa Fatimah Bintu Al-Hasan

Abokiyar zaman sa Farwah bint al-Qasim (en)

Yara biyu;

Jafar Ibn Muhammad

Sultan Ali (en)

da Ahali Zayd Ibn Ali (en).


KARATU:

Dukkan ilimin Zamani

Yaren sa Larabci

Malamin sa Mahaifinsa Ali Ibn Hussain (AS)

Ɗalibai biyu;

Ɗan sa Jaafar Assadiq (AS)

Abdur-Rahman Al-Awza'i (en)


AIKI:

Mai rawaitowa; wato “Rawi” (en)


IMANI:

Addin Musulunci 

Aqidar Shi'ah isna ashariyyah Khalifan Annabi a zamanin sa.


SHAHADAH: Madinah, 26 ga Janairu, 733

Makwanci Al-Baqiya'

Yanayin mutuwa (Shahadah ta hanyar Dafin guba).


MADOGARA:

Littafin wafiyatu Al-A'ayanu jizi'i na 3 shafi na 314,

Tarkiratu Huffaz jizi'i na 1 shafi na 124

da littafin Dala'ilu Al-Imamah shafi na 93.


©Abdullahi M Ali

Post a Comment

Previous Post Next Post