Offline

Sojojin Mamaya na Isra'ila sun kama mutane da dama a Jenin, Mazauna Isra'ila suna kai hare-hare


Dakarun mamaya na Isra'ila sun kama wasu matasan Falasdinawa hudu a ranar Talata daga garuruwan Qabatiya da Burqin dake kudu maso yammacin Jenin.

Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Wafa cewa, an gwabza kazamin fada bayan da sojojin mamaya na Isra'ila suka kai farmaki a garin Burqin da ke yammacin Jenin, tare da cafke Osama Hisham Khallouf bayan sun kai farmaki a gidansa.

A birnin Qabatiya, sojojin mamaya na Isra'ila sun kame Sami Ghoneim, da nufin tursasa 'ya'yansa biyu Ahmad da Mohammad da su mika kansu.

Sojojin mamaya sun kuma kama Mohammad Omar Al-Shami da Omar Hashem Kamil tare da kai samame gidan iyalan shahidi Habib Kamil.

Har ila yau sojojin mamayakan sun kai farmaki gidajen fursunonin da aka sako da dama, tare da yin barazanar kama su bayan yi musu tambayoyi, ciki har da Ahmad Rashid Kamil, da yayansa Mohammad (wanda suka lakada masa duka), Ibrahim, da Moamen, da Mahmoud Kamil, Saad Mohammad. da Mamoun Nasr Abu Al-Rub.

Sojojin mamaya sun kuma kai farmaki kauyukan Tora, Al-Tarm, da Nazlet Zeid a Ya'bad, inda suka kaddamar da mummunan bincike.

Kazalika sojojin mamaya sun kai farmaki garin Tammun dake kudancin Tubas, inda suka kai samame gidaje biyu a wurin.

A nasa bangaren, daraktan kungiyar fursunoni da ke Tubas, Kamal Bani Odeh, ya nuna cewa sojojin mamaya na Isra'ila sun mamaye garin tare da bincike gidajen shahidai biyu, Imad da Bakr Bani Odeh, tare da yi musu barna.

Ya kuma tabbatar da cewa an yi arangama tsakanin matasan Falasdinawa da sojojin mamaya, ba tare da an samu jikkata ko kama wasu ba.

A cikin wani yanayi mai alaka da shi, wasu mazauna haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hari kan motocin Falasdinawa a kan babbar hanya, kusa da kauyen Al Mughayyr, arewa maso gabashin Ramallah da yammacin ranar Litinin da ta gabata.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Wafa cewa ‘yan gudun hijirar sun far wa motocin da ke wucewa da duwatsu, yayin da jami’an tsaron suka tare hanya ta bangarorin biyu.

Source: Almaydeen

Fassarar: Freedom Fighters NG

Post a Comment

Previous Post Next Post