Offline

​Iran: Hukumar Leken Asiri Na Iran Ta Wargaza Wasu Kungiyoyi Biyu Masu Aikiwa MOSAD

Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran tanakalto majiyar hukumar tana fadar haka a jiya Talata. Ta kuma kara dacewa mutane 23 ne a cikin kungu gud na ma’aikatan na Mosad 13 daga cikinsu sun suga hannu, sannan babbansu wani ne wanda yake cikin daya daga cikin kasar Turai mai suna Siroos .

Labarin ya kara da cewa Siroos yana mu’amala da abokan aikinsa a cikin kasar Iran ta hanyar kafar sadarwa na Instagram da kuma wattsApp.

Labarin ya kammala da cewa an kama ma’aikatan MOSADS ne a biranen Tehran, Esfahan, Yazd, Azarbaijan ta yamma da kuma Golestan. Sannan an kwace kayakin aikin leken asirin da ke hannunsu.

Source:HausaTv

Post a Comment

Previous Post Next Post