Salon da abokan hamayyar jamhuriyar Musulunci ta Iran suka ɗauko don ƙoƙarin ruguzata ta hanyar farfagandar siyasa, sai dai basuyi Sa'a ba lokaci guda salon da suka ɗauka bayyi tasiriba yayin da suka ɗau mataki kai tsaye ta hanyar bayyana maitarsu a fili game da ƙiyayyarsu ga addinin musulunci ta hanyar fakewa da shi'anci
Yanzu haka sun sanja akalar salon nasu ta wani ɓangare kuma yayinda suke nunawa sauran Ɗaukacin Al'ummar musulmi Ahalussunnah cewa Iran tsastsaurar a ƙida kawai take amfani dashi take mulkar al'ummar ƙasarta ba musulunci ba ta hanyar tursasawa mata saka Hijabin ajikinsu domin rufe tsaraicinsu, sai sukayi amfani da wannan gaɓar wai hakan cin mutuncin ƴaƴa matane saboda haka sukayi amfani da mutuwar Ƴar Jaridar nan mai suna Mahsa Amini wadda ya faru a ƙasar kwanannan; wai shine silar fitowarsu tare da zimmar nemawa ƴaƴa mata ƴancinsu a matsayinsu na masu kare haƙin mata.
Lokaci guda Allah ya toshe musu basira akan wannan salon makircin nasu da suka ɗauko yanzu, sun manta cewa kowace Aqidah ta musulunci an halarta hijabi a mace bugu da ƙari shinema siffar muminan mata a kowane janibi cikin Aqidun musulunci, wadda in muka duba hatta Aqidun kiristanci ba'a haramta sa hijabiba a ciki ba a salima addinin nasu akwai Al'adar rufe tsaraici acikinsa.
Sanin kowane ga wadda yake bibiyar siyasar duniya cikin kwana kinnan Manyan ƙasashen kafirai sun ɓude fiƙoƙinsu akan ƙasar jamhuriyar Musulunci ta Iran wato (Islamic Republic of Iran) Kamar yadda ake ganin cikin kwanakin nan da muke ciki zamuga manyan kafafan yaɗa labarai na abokanan hamayyar Iran ɗin irinsu #BBC Hausa, #RFI Hausa, #VOA Hausa tare da sauran wasu kafafen sa darwa na turanci suna yawo da wasu sabbin rahotanni game da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ɗin cewa an cigaba da zanga-zangar ƙin jinin hijabi a ƙasar kamar yadda ya faru jiya a ƙasar Amurka a bakin ofishin (White House) cikin birnin Washington wai an samu wasuma sun fito zanga-zanga game da Iran ɗin suma suna nemawa matan Iran yancinsu daga ƙasar Amurka saboda rashin kunya.
Idan musulmai suka cire aqidanci tare da ƙabilanci sukayi nazari akan wannan al'amarin mutum zai iya tambayar kansa cewa menene hadafin wannan zanga-zangar Iran ɗin da har ta dangana zuwa ƙasar Amurka zuwa bakin White House wai da taken nemawa matan Iran Ƴancinsu? Manufar tasu a bayyane take shine a soke saka #hijab a ƙasar Iran ma'ana rayuwar rufe tsaraici mata su koma rayuwar da ta buɗe tsaraicinsu a fili.
©Abdullahi M Ali
Tags
Resistance News
