Tir da mutumin da yake da fuskoki biyu da harsuna biyu (munafuki). Yana yabo ga dan uwansa (DAN UWA NA ADDINI) a gabansa kuma idan ba ya nan sai ya koma ya ci NAMAN SA (GULMA) da yi masa kazafi. Idan ya samu (wani abu) sai ya yi hassada da shi, idan kuma WAHALA ya same shi, sai ya taFI ya bar shi (Ba ya taimakonsa).