Offline

Sojojin mamaya na Isra'ila sun kai hari kan masunta da manoma a Gaza

Dakarun mamaya na Isra'ila (IOF) sun kai hari kan manoma da masunta Falasdinawa a zirin Gaza da safiyar Juma'a.

Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wuta da manyan bindigogi kan wasu jiragen ruwan Falasdinawa uku na kamun kifi bayan da suka yi musu kawanya a lokacin da suke tafiya a gabar tekun kudancin Gaza. 

Sojojin na IOF sun kuma bude wuta da manyan bindigogi kan manoman Falasdinawa da ke kula da filayensu a garin Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza. 

Kungiyar ta IOF a kullum tana kai hare-hare kan manoma, masunta, da kuma makiyaya a yankin Zirin Gaza, inda hakan ke janyo hasarar rayuka da asarar dukiya. 

Source: Cibiyar Watsa Labarai ta Falasdinu

Post a Comment

Previous Post Next Post