Offline

Jibril Usman Sarki: Jigo A Fagen Gwagwarmaya da Neman Ƴancin Raunana.


Abin da matukar bacin rai da sosa zuciya yadda jini ke zuba kullum a kasar mu Najeriya, rayukan raunana ya zama bai da daraja awajan mahukunta, masu fafutukan nema ma raunana ƴanci suma rayukansu bai tsira ba irin su Jibril Usman Sarki.

Jibril Usman Sarki ɗan Gwagwarmayar neman ƴanci ne ga wanda aka zalunta ba tare da nuna banbancin addini ko kabila ba. Yana ɗaya daga cikin ginshikai a tafiyar ƙungiyar neman ƴanci na 'FREEDOM FIGHTERS NG'. Shike kula da shafin Twitter na @f_fightersng wanda ke wallafa rahotannin yadda ake cin zarafi tare da kashe mutane a kasashe irin su Ƙasar Palestine, Yemen, India, Afghanistan, Najeriya da sauran su. Harwala yau, yana wallafa rubutu daya shafi zalumci da danniya a shafin neman ƴanci na www.freedomfightersng.com .

Jibril Usman Sarki fursuna ne a gidan yarin Kuje dake Abuja yana jiran shari'a a gaban mai shari'a Suleiman Belgore na babban kotun tarayya dake Abuja bisa zarginsa da shiga jerin gwanon neman ƴanci ga Jagoran Harkar Musulumci a Najeriya wato Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a Muzaharar #FreeZakzaky da ta gudana a ranar 22/07/2019 a Sakatariyar Tarayya, Abuja. An kama Jibril Usman Sarki ne tare da wasu mutane 62. Acikin mako guda da kama su, wasu masu jerin gwanon neman ƴancin 3 sun mutu a hannun ƴan sanda na SARS saboda gallazawa da rashin kula da lafiyarsu, Sannan ƴan sandan sun kai gawarwakin 3 asibitin gundumar Asokoro. Ya zuwa yanzu dai ba a kai gawarwakin ga iyalansu ba tsawon shekaru 3.

Cikin Daren Talata 05/07/2022 Tawagar Sojojin Najeriya da aka aike zuwa gidan yarin Kuje bayan kai farmaki gidan yarin da ta faru, tsananin harbi daga maharan ya tilastawa daruruwan fursunonin ficewa daga harabar gidan yarin domin tsira da rayukansu.

Don haka sai Jibril Usman Sarki tare da wasu fursunonin suka fice daga gidan yarin. Kimanin sa'o'i 2 da faruwar lamarin, fursunonin sun ga wasu motocin Sojojin Najeriya suna sintiri akan titunan garin Kuje; sun yanke shawarar ganawa da Sojojin da neman kariya da taimako don komawa gidan yarin da kan su inda ake tsare da su.

Shaidun gani da ido sun tabbatar cewa, fursunonin da ke cikin ruɗani sun yi ta ihun cewa "Mu ƴan fursuna ne", amma maimakon taimako sai Sojojin suyi ruwan harsaisai a kansu wanda hakan yayi sanadiyyar raunatawa tare da kashe mutane da dama ciki har da ɗan uwa Jibril Usman Sarki. Bayan harbe-harbe, Sojojin sun ajiye waɗanda suka jikkata da gawarwakin waɗanda suka kashe a Hannu hukumomin gidan yarin.

Da wannan mu ke yin Allah wadai da kisan abokin aikin mu Jibril Usman Sarki, muna kuma jajantawa duk Wanda wannan kai farmaki ya rutsa da su.

Sannan cikin jimami, muna mika sakon ta'aziyyarmu ga ƴan'uwa, dangi da abokai, a lokaci guda muna rokon Allah yayi masa rahama ya karbi shahadarsa.
Hakika ba mu shaidi komai ba awajan Jibril Usman Sarki sai kyawawan ayyuka abin koyi.

Muna rokon Suratul Fatiha zuwa ga ruhinsa.

–FREEDOM FIGHTERS NG
10th July, 2022

Post a Comment

Previous Post Next Post