Offline

Auren Sayyada Fatima Zahra da Imam Aliyu bn Abi Talib Salamullahi Alaihima.


Aliyu Samba 

Allah SWT ya ba Musulunci nasara a yakin Badar a shekara ta 2 bayan hijira. Bayan wata biyu da yaƙin Badar aka daura auren Sayyada Fatima Zahra diyar Annabi Muhammad Mustafa da Imam Ali dan Abu Talib Salamullahi Alaihima.

Sayyada Fatima Zahra tana da shekaru biyar kacal mahaifiyarta Nana Khadija AS tayi wafati, daga nan kuma mahaifinta, Annabi Muhammad Mustafa SAWA, ya dauki nauyin aikin uwa a gare ta. Wafatin mahaifiyarta ta haifar da giÉ“i a rayuwarta amma mahaifinta ya cike wannan giÉ“in da soyayyarsa, kaunarsa da kuma jinÆ™ansa gareta. 

Annabi Muhammadu SAWA ya ba da cikakkiyar kulawa da tarbiyya ga Sayyada Fatima har sai da ta zamo abar misali a tsakanin mata. Kamar yadda Annabi ya zamo shi ne abin koyo ga dukan Musulmi, Sayyada Zahra ta zama abar koyi ga musulmai,  kuma abar duba da koyin Æ´a mace a Musulunci. Sayyada ta zamo a daraja ta daya cikin ibada da biyayya ga mahalicci, kuma tsaftatacciya tsarkakakkiya a duniya da kiyama. A É—abi'a, ta yi kamanceceniya da mahaifinta, har ta zamo tamkar makwafin sa a idanun muminai a siffa da kamala. 

Saboda tsananin biyayyar ta da bautar Allah, Fatima Zahra ta kai matsayi mafi girma a wurin Annabi SAWA, Allah ya yi mata mafi girman daraja, kuma Manzon Allah (saww) a nasa bangaren ya nuna mata alamar girmamawa mafi girma, wadda ba ya nuna wa wani namiji ko mace a kowane lokaci a rayuwarsa.

Lokacin da Fatima ta kai minzalin aure, wasu sahabbai biyu sun nemi auren ta a wajen mahaifinta. Sai dai ya kau da kai daga gare su yana mai cewa;

"Wannan al'amari na auren Fatima 'yata yana hannun Allah ne da kansa, kuma shi kadai ne zai zabar mata".

Allah ya bayyana zabin Sa, Ya zabi bawanSa Imam Ali ibn Abi Talib ya zama Mijin diyar MasoyinSa Annabi Muhammad Mustafa SAWA. Allah ya hukunta auren Sayyada Fatima bint Muhammad da Imam Ali ibn Abi Talib.

Bayan wata biyu da yakin Badar, watau a cikin watan Zilqa'ad (wata na 11) na shekara ta 2 bayan hijira, Imam Ali ya je Æ™afa da Æ™afa wajen Annabi Muhammad Mustafa SAWA ya ce: 

“Ya Manzon Allah, ka rene ni a matsayin danka. Ka lullube ni da baiwarka, da karamcinka da kyautatawarka, hakika bana binka bashin komai a rayuwata, rayuwata fansa gareka, a halin yanzu ina neman wani alheri daga gare ka''

Manzon Allah SAWA ya fahimci abin da Imam Ali yake so ya ce, take fuskarsa mai daraja ta lumshe cikin murmushi, sannan ya umurci imam Ali da ya jira kadan ya samu amsar diyarsa Fatima. Yana shiga gidan, ya shaidawa Fatima cewa Ali yana neman aurenta, ya tambaye ta mece ce amsar ta. Tayi shiru ta sunkuyar da kai alamun yarda da kuma kunya, wannan shirun ya fassara ta a matsayin amincewar ta, sannan ya koma ga Ali, ya sanar da shi cewa ta amince, ya kuma ce masa ya shirya domin a É—aura musu aure.

A ranar karshe ta Zilqa'ad (wata na 11) Annabi Muhammad Mustafa SAWA ya gayyaci Muhajirai da Ansar (Mutanen Makkah da Madina), domin halartar liyafa ta bikin auren diyarsa da kuma wasiyyin sa. A wannan lokaci Annabi SAWA ne ya zama mai masaukinsu. Da dukkan baqi suka iso, kuma suka zauna, sai Annabi SAWA  ya sake neman amincewar diyarsa na aurenta da Ali binu Abi Talib sannan ya daura musu aure washe gari daya ga watan zilhijja. 

Bayan yabo da godiya ga Allah, Annabi SAWA yayi hudubar aure ya ayyana Ali da Fatima a matsayin miji da mata, kuma ya yi addu’ar tabbatar alkairi da albarka a gare su cikin rayuwar auren su. Dukkanin bakin da suka zo sun cika da farin ciki tare da taya Annabi SAWA murnar wannan rana mai albarka. Anyi walima da naman rago, burodi, 'ya'yan itacen dabino da madara wanda aka raba shi tsakanin mahalarta walimar auren, ba shakka an ci an sha an kuma yi farin ciki a wannan rana.  

Bayan 'yan kwanaki, watau a watan Zilhajj (wata na 12) Nana Fatima Zahra ta yi bankwana da gidan Mahaifin ta zuwa gidan mijinta. Mahaifinta Annabi SAWA shi ya taimaka mata wajen hawan rakuminsa. Madina ta cika da sautin kabbarar mutane cikin farin ciki. Salmanul Farisi shine ya rike ragamar rakumin, yana tafe yana rera karatun Alkur’ani. Manzon Allah (SAWA) ya na ta gefe daya na rakumin, sai Hamza Zakin Allah a daya bangaren.

Duk matasan mayaÆ™an Banu Hashim a wannan rana sun yi hawa don rakiyar amarya, É—auke da takubba masu ado da kyalli. A bayansu akwai matan Muhajir da Ansar, bayansu kuma Muhajirai da Ansar maza na biye da su, suna ta rangaÉ—o ayoyin Alkur'ani mai girma cikin yabo da nuna girman Allah SWT, sannan kuma suna biyowa da gunjin kabbara cikin farin ciki. 

Wannan tawagar mai daraja da ta rako masu daraja ta biyo ya babban masallacin Madina, sannan ta tsaya a inda suka nufa wato gidan ango Imam Ali ibn Abi Talib. Annabi SAWA ya taimaki diyarsa Sayyada Fatima wajen saukowa daga rakumin. Ya rike hannunta, ya sanya shi a hannun mijinta, sannan ya tsaya a bakin kofar gidan, ya yi addu’a kamar haka:

“Ya Allah! Ina mika lamarin Fatima da Ali a hannun ka, bayinka masu kaskantar da kai gareka. Ka kasance majiÉ“incinsu, ka Albarkace su, Ka yarda da su, kuma Ka ba su falalarka da rahamarka da mafificin ladan ka gare su. Ka kyautata rayuwar aurensu, kuma Ka tabbatar da su a cikin soyayyarKa da hidimarKa.”

Hakika wannan rana ranar farin ciki ce a rayuwar Annabi Muhammad Mustafa SAWA, a yadda yaso ace matarsa kuma aminiyar sa  Nana Khadijah AS  ta kasance tare dashi domin su shaida wannan babbar rana ta bikin diyarsu.

Bayan 'yan kwanaki Manzon Allah SAWA ya kira 'yarsa, ya tambaye ta yadda ta sami mijinta. Ta ce ta same shi mafificin abokin zama wajen yawaita ibada da biyayya ga Allah. Daga baya, ya tambayi Ali yadda ya sami matarsa, sai ya ce ya same ta ita ce abokiyar zama mafi kyau wajen yin hidima ga Mahalicci. Mafi girman lokutan rayuwa ga mata da miji su ne waÉ—anda idan suka tsaya gaban Ubangiji, suke shagaltu da yin addu'a gare shi. Wannan shine babban makamin da ke gidan Imam Ali da Mawlatiy Fatima Salamullahi Alaihima.

Tsakanin Ali da Fatima Zahra, an sami ainihin hakikar maslahar zamantakewa. Dukansu sun samu reno da tarbiyya ne daga shugaba Muhammadu Mustafa SAWA da Nana Khadija-tul-Kubra AS, sun yi tarayya da manufofi irin na iyayensu, kuma sun sa hidima ga Allah gaba da komai. Babu wani sabani a tsakaninsu, tunaninsu da maganganunsu da ayyukansu, duk “al-Qur’an ne ya tsara su”. Don haka aurensu ya kasance cike da kamala da farin ciki kamar yadda auren Annabi Muhammad da Nana Khadija ya kasance. 

Kamar yadda aka ambata a sama, babban abinda yake yardar da Nana Fatima shi ne ta hidima wa Allah. Ta kasance mafi yawan lokutanta a cikin addu'a. Babban abin jin daÉ—inta na biyu shi ne ta sauke nauyin iyalin ya. Allah ya azurtata 'ya'ya hudu - na farko maza biyu sai kuma mata biyu. 

Sayyada tana niƙa hatsin da mahaifinta ya ba ta daga cikin sadakinta, ta hada ƙulli tayi musu burodi. Yawan niƙa wannan hatsi kowace rana ya taba sanya kumburi a hannunta, amma ko kadan ba ta taba kokawa mijinta ko mahaifinta a kai ba, kuma ta na gudanar da duk aikinta na gida cikin farin ciki.

A duk sanda ayyukan gida suka yawaita ga sayyada Fatima Zahra, ta na samar wa kanta farin ciki cikin ambaton Allah yayin gudanar da aikin. Littafin Allah (Alqur'ani) shi ne abokin zamanta a koyaushe. Yana mantar da ita wahalar aikin yayin da take karanta wasu sassa na wannan littafin. A duk lokacin da zata sa 'ya'yanta su kwanta bacci, tana karanta masu zaɓaɓɓun ayoyi daga cikin Alqur'anin dan ya zama abin nishadantarwa a gare su.

Ƴaƴan Sayyada Zahra sun taso suna jin Alqur'ani mai girma tun suna kanana. Ta ɗora Maganar Allah a kan su tun daga ƙuruciyarsu. Ta hanyar irin wannan tarbiyya, Kur'ani da 'ya'yan Fatima Zahra suka zama abokan tarayya marasa rabuwa har abada.

A cikin wannan shekarar, wato a shekara ta 2 bayan hijira, aka sunnanta wa musulmi sallar jam'i a ranakun hutu guda biyu wato Idil-Fitr da Idin layya.

Allah ya bamu albarkacin su. Ameen.

Post a Comment

Previous Post Next Post