Ko me yasa wasu daga cikin masu ra’ayin cewa addinin Musulunci ba zai iya yin iko da kasar nan ba su ke fassara “Shari’a” da wani bangare na ta- horo (punishment)- su kawar da kai daga sauran bangarorin ta? Ko kuma su fassara ta da irin fassarar maqiya addini- irin fassarar da turawa su ka yi wa shari’a a litattafan su- duk da kasancewar su wadanda ba ‘practicing’ shari’a din ta su ke yi ba?!
Idan mutum ya karanta litattafai da takardun da turawan yamma da maqiya addini a ko’ina a fadin duniya su ka rubuta akan shari’a, zai ga su na yin magana ne akan horo kawai, don a wautar su horo (punishment) shi ne shari’a din ma baki daya. Idan ance shari’a kai tsaye ana nufin horo (punishment) ne kawai, a rashin kan gado irin na su. Su na dauka “Shari’a” ma’anar ta kai tsaye kawai shi ne “horo(punishment)”.
A wasu litattafan kuma su na fassara shari’a da ayyukan wadanda ake kira da masu tsattsauran ra’ayin addini (fundamentalists) da kuma qirqirarrun ‘yan ta’addar da su ka samar irin su ISIS, Alqa’eeda, Boko Haram, da sauran su; duk da a zahiri ayyukan duk wadannan ya saba ma haqiqanin shari’ar addinin Musulunci. Amma dai yanzu ma sai ka ga idan an tashi magana kan rashin dacewar tsarin addinin Musulunci a kasa irin Najeriya, sai wasu su ke fassara shari’a da haka, duk da a zahiri (har ga zuciyar su) sun san ba haka take ba.
Shari’a ita ce dan Adam baki daya, abun da ta kunsa kamar wani ‘life code’ ne na rayuwa; ta kunshi komai da komai da dan Adam ke bukata wajen gudanar da rayuwar shi. Ta na da bangarori daban-daban, daga cikin su akwai horo (punishment) wanda wani dan karamin (bangare ne daga ciki) don kiyaye qa’idoji da kawo saiti (order) a zamantakewa da rayuwar dan Adam baki daya.
Shari’a ta kunshi hatta yanda mutum zai ci abinci, yanda zai sha ruwa, yanda ya kamata ya yi mu’amala da sauran al’umma, yanda ya kamata dabi’ar shi ta kasance, yanda mutum zai yi bacci, yanda zai tashi daga bacci, yanda zai yi ibada, da komai da komai! Ko da Allah (T) Ya halicci dan Adam ba wai ya bar shi kara zube ba ne, ita shari’a ita ce ke saita rayuwar mutum.
Abun mamaki ne da an fara maganar ya kamata ya zama tsari na shari’ar addinin Musulunci ne ke tafiyar da kasar nan, sai ka ji wasu sun fara batun guntule hannu, bulala, jefewa da dutse (tsakuwa), qaqabawa mata sanya Hijabi dole, take haqqin mata, da sauran su.. Ah ah! To wa yace horo (punishment) din nan da ake ta fassara shi yanda aka ga dama shi ma, shi ne yake nufin shari’a din baki daya?
Me yasa wasu daga cikin masu wancan ra’ayin ke ajiye bangaren shari’a da ya shafi ibadat, mu’amala, dabi’a, gina al’umma, kyautatawa da sauran su?! Zan sake maimaitawa, horo (punishment) ba shi ne shari’a ba, wani bangare ne na shari’a (wanda ya ke) don kiyaye dokoki. Bisa dabi’a dan Adam ya na bukatar abun da zai saita shi, ya dora shi akan tsari, ya samar da ‘order’ da gudun ketara iyaka a al’amura na yau da kullum.
A ajiye batun tsarin addinin Musulunci a gefe, bari na yi wani tambaya: akwai wani tsari a duniya kaf wanda babu bangaren horo (punishment) a cikin shi? Kama daga tsarin gargajiya na imani da ababen bauta da babu su a zahiri (ancient mythologies), zuwa tsarin da mutane a yanzu ke kallo a matsayin mafita irin su jari-hujja (capitalism), gurguzu (communism), da duk ma wani tsari a duniyar nan a tarihi; don Allah wanne ne daga ciki babu dokoki da kuma wani bangare na horo (punishment) da aka samar don kiyaye wannan dokokin da gudun ketare iyaka a tsakanin al’umma?!
Me yasa kuma da an fara batun shari’ar addinin Musulunci sai wasu su yi caaaaa, su fara batun horo (punishment) kawai, su kyale sauran bangarori; kai kace daman a sauran tsarikan da ake ganin su ne mafita kamar su tsarin ‘secularism’ babu dokokin horo (punishment) a cikin su..
Wannan matashiya ce, akwai ci gaba, idan Allah Ya yarda.
- Najeeb Maigatari (谦虚)
10/06/2022
Tags
Makaloli