- Sayyid Zakzaky (H), a lokacin wafatin Sayyida.
Wai me ya sa ita Sayyida Zahara (s.a) ba ta da Hadisi ne? Alhali kuma tun tana Makkah akan ji ma Babanta yaji ciwo, ya dawo gida har ta wanke masa? Kuma suna da ruwaya a kan haka nan Saboda haka ta zauna da Babanta a Makka. Ya yi hijira tare da ita. Kodayake shi ma sun rufe Sun murguda tarihi. Yanzu in ka tambayi mutum, wai Manzon Allah (S) ya aka yi ya shiga Madina, yayin da aka yi wakar Dala'al Badaru Alaina'? Sai su ce ya shiga ne da shi da Wane. Har ma suna yin hoto haka nan, rakuma biyu, da na Annabi da na Wane.
Alhali sam ba haka bane! Sam Annabi bai shiga Madina da Wane ba! Ya yada zango ne a Kubah, kuma yana nan a ruwayarsu; a nan aka yi Juma'ar farko. Ina Kubah, ina Madina? Ya za a ce an ce an gano ga shi can ya shigo, alhali ya yi kwanaki a Kubah? Sai dai in zuwa Kubah ne. Ya yada zango a Kuba, ya jira Amirul Muminin da iyalansa, "kawafilul Fawadim." Daga cikin su akwai Fatima 'Yarsa da Fatima bintu Asad (Uwar Amirul Muminin), da kuma Fatima bintu Hamza, da kuma ita Ummu Aiman din nan, tana cikin su. Da kuma Jagoransu Amirul Muminin, wanda ya zo da su. To, da su ya shiga Madina, ranar Dala'al Badaru Alaina'
To, ka ga ta kasance tare da Babanta
har ta yi hijira tare da shi, ta shiga Madina tare da shi, ta rayu tare da shi. Amma ba ta ji komai ba wajen Babanta? Kuma ba a ji komai a wajenta ba? Wala'alla su ce, ai ba ta dade ba bayan Babanta ba ne. To, ko da ba ta dade ba, wadansu na kusa da ita ba su ji wani abu ba daga gare ta? Kamar ita Ummu Aiman din nan, ai ta dade bayan Annabi. Har an ce su wane da wane din nan sukan je su gaishe ta, ko? To, tunda ta zauna da Sayyida Zahara, ita ba ta ji komai ba da ta ce ta ji wajen Babanta? Ba ruwayar Sayyida Zahara (AS). Hatta a littafin da ake ce masa 'Asahhul Kutub ba'adal Kur'an, to ba ruwayarta ko kwara daya. Wannan abin da ya kamata mutum ya yi tunani kenan. To, ita ba ta ji komai ba ne wajen Babanta?
To 'ya'yanta kuma ba su ji mamansu ta ce kaza ba ne? Don Hasan da Husaini ai sun girma. Shi Imam Husaini ya kai shekara hamsin da wani abu, gaf da sittin. Shi kuma dan uwansa ya kai gafda Hamsin. To, kuma ai Amirul Muminin Maigidanta, ya rayu bayanta shekara kusan talatin. Kuma 'ya'yan nan nata, bayan Amirul Muminina da shekara goma, wafatin Imam Hasan. Bayan nan kuma da shekara kamar Ashirin, wafatin Imam Husaini. To, su kuma ba su ji komai ba ne wajen Mamansu? Kuma Sayyida Zainabul Kubura kuma ta rayu bayan Hasan da Husaini. Ita ba ta ji komai ba ne wajen Mahaifiyarta? Ita Sayyida Zainabul Kubura, in ka ce mata 'tape-recorder ka bata bakinka. Don ruwayar 'Fadakiyya, ita ta ruwaito hudubar Mahaifiyarta. Shekararta shida lokacin, duk abin da Mahaifiyarta ta fada gaba daya ta nada ta fada. To, ai ita ta rayu. Ka ga kenan ba za a rasa ruwayar Sayyida Fatima Zahara ba kenan ko? Ko da daga wajen Fidda, ainihin kuyangarta, ko Ummu Aiman, wannan dattijuwan da ta ga Annabi tun yana yaro ta kuma ga har wafatinsa, ta rayu bayan wafatinsa, ko kuma 'ya'yanta ko makwabta.Duk a rasa duk ruwaya dinta? To, shi ma ka ga muhallin walakin ne. Me ya sa ba ta da Hadisi? Ka ga hankali ya kamata ya ce: to ya aka yi haka nan ne? Ka ga wani 'area' na walakin ke nan. Saboda mene? Dole ya zama ba ta da hadisi mana, domin in aka fado hadisin, ai wadà nsu abubuwa za su dago.
Shi ko magance abu da bizne shi, da cewa a daina kallon sa, kar a fade shi, to guje ma gaskiya ba shi ne maganin ta ba. Kamar mutum ne ya dodana ma nakiya wuta (nakiyar da ake fasa dutse), sai ya sa masa matashi ya zauna abin sa. Ya zauna lafiya. Har wutan ta kai nan, ka ji daram! To, ainihin bizne gaskiya ba mafita ba ne, don tana nan.
Kokarin da aka yi a ce, to a yi shiru, a daina maganar Sayyida Fatima, kar a fada, don in an fada za a dago da abubuwa, to fa ba magani ba ne, don ya bar mu da walakin.
Wannan walakin din zai sa a ce; meyasa ba ta da hadisi? Malam Wane me ya sa ba ta da hadisi? "Wallahi shi.... Ai ta mutu da wuri ne, bayan Manzon Allah ta mutu. To, 'ya'yanta ba su ji komai ba wajenta? Su sun mutu da wuri ne su ma? Ba su ji komai ba kenan, lokacin wajen mahaifiyarsu ke nan ba ko? Kila sun ji. To, ba su fada ba ne? Kai ya zai zama ba su fada ba? To, kila dai ba a rubuta ba.
Fadi gaskiya, an ki a fada ne! An ki fada ne! To, me ya sa aka ki fada? Sai ran da ka ga Hadisan Sayyada Zahara za ka san cewa dole ne ko su boye. Domin da da hadisan Sayyida Zahra, ba ka bukatar Hadisan su wance da wance. Don ta fi su kusa da Annabi. Don ita bangaren jikin Annabi ne. Me ya sa ba a san inda aka bizne ta ba? Shi ma kowa, sai ya yi maka shiru. Ka ga ashe da walakin a rasuwarta kenan ko? Ka san ya kamata duk a san da rasuwarta, kuma duk ya zama wani abu ne karara, ansan shi. Jama'a za su hadu. Ko da ma matsayinta 'perhaps' kawai "yar Manzon Allah ce, 'Perhaps'.
Abin da muke cewa; ita Sayyida Zahra matsayinta ya wuce 'yar Manzon Allah kawai. Tana da wani matsayi ne na musamman. Kuma akwai abin da ya 'ahhala ta' ga wannan.
Daga cikin yunkurin da suke ta kokarin su nuna, sukan ce kawai ita 'diya ce ta Annabi, kawai, shi ke nan an gama. Don haka ma suka ce akwai wadansu diyoyin ma. In Amirul muminina ya auri daya, to Wani ma har biyu ya aura. Har ma wai Annabi ya ce; da yana da ta uku ma da ya ba shi. Da ya zama zee salasatu anwar ba Zinnuraini' ba. Zee anwarun salasa. Amma wani abin mamaki shi ne, kuma ba su fadin komai game da wadannan, illa iyaka kawai su ce an yi su, an gama. Amma Sayyida Zahra ta ki biznuwa musu. To, wannan hujjar hankali ke nan, zai sa ka fi tunani.
To, in aka zo aka tono ruwaya, ka gwama da hankalinka. Misali, me ya sa ba ta da hadisi? Sai kowa ya yi shiru. Kuma ba za yiwu ya zama ba ta da hadisi ba, ko? To, ran da aka zo aka dago hadisanta, ka gani, za ka ce yanzu na gano dalilin da ya sa aka rufe. Alal misali, akwai wani ruwayar hadisinta da na gani, ta ruwaito dangane da Kiran Sallah, da isnadi, an wane, an wane, daga Sayyida Fatimatuz Zahara, ta ce; "Yayin da aka yi Mi'iraji da Mahaifina, da ya je saman bakwai (Sidiratul-Muntaha), sai ya ji kiran sallah. Sai ya ji ana biyuntawa shi ne, ya ji kuma ana ifradin Ikaama. (Kodayake wannan ifradin wasu suna fahimtar sa kamar ana yin kwara dai-dai ne). In ka ce, "Ashhadu an la ilaha illallah ka yi shiru, ka ce Ashhadu an la ilaha illallah, ka biyuntawa. In ka ce "Ashhadu an la ilaha illallah-Ashhadu an la'ilaha illallah ka gwama. "Allahu Akbar Allahu Akbar ka gwama. Ifradi ke nan. "Alahu Akbar biyudanta. Ma'anarsa kenan. Ba yana nufin ana cewa irin na Mazhabar Malikiyya ne ba "Allahu Akbar, Allahu Akbar, Ashhadu an la'ilaha illallah, Ashhadu anna Muhammadar Rasulullah, hayya ala sallah, hayya alal fala kad kamatus-Salah.. Wasu suna Kad kamatus Salah' sau biyu, sauran kuma 'ifradi." To, ifradi' yana nufin biyuntawa ne amma a Allahu Akbar, ka raba, ka gwame, sai ya maishe shi lfradi. To, sai aka samu ruwaya a wajenta cewa; kiran sallah da Manzon Allah ya yi Mi'iraji ya ji ana yi a 'Sidiratul Muntaha', sai yaji kiran sallah, yaji ikama."To, ka san in ka kwatanta wannan da cewa ainihin da aka gina masallaci ne a Madina, aka yi 'meeting, Annabi ya ce, to ga shi mun gina Masallaci, ya
za mu yi mu kira mutane izuwa ga Sallah Annabi yana neman shawara ne. Allah (T) bai ce "Dinuhum shura bainahum ba! Ya ceamruhum ne! Amruhum,' ma'ana tafi da mulki. Shi ne 'amr anan. Tafi da mulki. Meye ma'anar "Amr' a nan? Ku gaya mini me na fada yanzu? Tafi da mulki. Gudanar da mulki ba al'amari ne da mutum shi kadai yake tafi da shi ba, 'shura' ne. Shi ne ma'anar 'Amruhum shura bainahum Amma bai ce 'Dinuhum shura bainahum' ba. Addinihum Wahayi, wahayi ne. Ba suna tattaunawa ne su ce raka'a nawa za a yi ba? Kamar yadda Musailamatil Kazzab aka ce ya kira mutane ya ce, to, nawa ne za a sa sallah? Aka ce, to shi dai Muhammadu dai biyar ne. Ya ce; eh ya cika yawa nasa. Suka ce Ya Nabiyallah,' to a yi uku kenan? Ya ce 'Uskut al-wahayi Yanzul'. Kawai sai ya ce Uhhm, sa'aj'aluha lakum isnain'. To, ka gani. Ka ga shi addinin ma yana tattaunawa ne, yana da yan rahoto, in sun je sun ji Annabi, sai su zo su gaya masa. Su ce an saukar da Suratul Fil. Shi ma sai ya ce, ai shi ma an saukar masa da nasa: Al-filu fil, wama adraka mal fil? Lahu Jismun kabir, wa khurdumin dawil.. Dinihum shura bainahum' kenan. Amma addinin Allah, ya za ayi kiran sallah, a yi masa shawara? Adadin raka'o'i shawara aka yi? Ko an yi wahayi ne? Azumin Ramadan, shawara aka yi? Ko ko an saukar ne? Addini ana saukar da shi ne. Ba a ce Dinuhum shura bainahum' ba, 'Amruhum', tafi da gwamnati, gudanar da gwamnati. Ba doka ba, ba hukunci ba. In za ku gudanar da abu, meye maslaha? To, shi ne ake shawara, a babin maslaha, ba a babin shari'a ba. Shari'a ba muhallin shawara ba ne. Ba a mata ana shawara. Umurni ne, bi za ka yi, ko ka butulce. Ka zabi daya. Ko ka bi, ko kar ka bi. Amma ba ka da iko ka ce kana da shawara. Kana da shawara, me ya sa Allah ya sa a rika Sallah kaza? Ga ka da shawararka! Wa ke bukatar shawararka a nan'? Ba bukata! To, shi kenan dai.
To, kun ga kenan, in kun kwatanta da wanda aka yi shawara, wani ya ce to, a hura kaho? Ya ce a'a, ai Yahudu Raho suke hurawa.
To, a yi Gwarje? Ai kuma Kirista gwarje suke. Nasara suna Gwarje ne. To, ya kenan? Sai aka tashi ba a tsai da matsaya ba, Da daddare kawai, sai wani ya yi mafarki, ya ce ya siyo gwarje a kasuwa, sai wani ya tambaye shi; me za ka yi da Gwarje? (a mafarki fa), sai ya ce; ai zan rika karkada ma mutane ne (Gwarje shi ne kararrawa irin wanda ake a coci), Garan-garan garan! A zo ai Sallah. Sai ya ce; zan kadawa mutane ne. Sai ya ce; in koya maka abin da ya fi alheri daga wannan? Ya ce mene? Sai ya yi masa kiran Sallah. Da safe sai ya gaya ma Manzon Allah ya ce ga abin da ya ji. Sai ya ce, to koya ma Bilal, tashi ka kira. Bilal yana kira kawai, sai wani ya zo yana jan rigarsa. Ya ce, na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya, ni ma na yi irin wannan mafarkin, sai dai wancan ya riga ni fada ne. Ko ya aka yi ya san an yi mafarki ne, ya zo, ko riga ma bai saha vana jan ta ban sani ba.
To, ka gani, kwatanta wannan in aka ce maka wahayi ne, Sayyida Zahara ga shi ta ce Babanta ne ya ji kiran Sallah a sama, ga shi kuma yadda ya ji ake kiran sallan, ga yadda ake Ikama' din. Ka ruwaito wannan, alhali kuma wancan ruwaya din sahihi ya ce shawara aka yi? Wanne za ka dauka ke nan? Na Sayyida Zahra, ko kuma na 'Asahhul kutubul musannafa'? Sahihi ya ce, shawara aka yi. Sayyida Zahara ta ce an ji ne a sama. Wanne ne abin dauka? Na Sayyida Zahara! To, ka gani. Ka ga in an dauki wannan, wancan me za a yi masa? To, ka gani? Da ruwayoyi daban-daban na Sayyida Zahara, wanda in za a dauka dole a bankadar da abin da suka gina mutane a kai. Saboda haka dole a ce ba ta da ruwaya. Shi ne dalili, ba wani abuu ba.
Kuma 'zulama' dinta, wanda ya 'ahhalata' ga wannan babban darajar, ta sha wahalar da ta daure. Ya zama dole shi ma su yi shiru, saboda wanda suka zalunce ta sune aka ce sune addini. To, amma gaskiya fa, ba fa zaa dinga rufe ta ba. Na'am, mu mukan yi abinmu muna sakayawa, saboda mene? Muna so mutane su sa hankalinsu da basirarsu. Amma wasu sukan daie fito su yi maganganu, ka ji Sun ce, "ka san wa suke nuti ya yi wannan'? To, wallahi suna nufin wane ne. La ilaha ilallahu, yanzu wane ne zai yi kaza? To sai ka ji su an ji a bakinsu. Na wani Wawan gari, aka ji yana cewa; Wallahi abin da suke cewa an yi ma Sayyida Zahra, abin da suke cewa wai an yi mata, wallahi in ka ji wanda ya yi mata, za ka tabbatar arne ne ya yi. To, amma sai suka ce Wane ne. Sai na ce to, ka ji kai ka fadi sunansa ko? Kai ne dai aka ji a bakinka Amma dai ba mu ba. Wajensu aka ji. Dalili, tunda kai ka dauka addini ne wannan, to, dole ne ya zama, sai mu sa maka hankali domin ka fahimta. Yawwa!
Da yake lokaci ya dan kure manaa yanzu, insha Allah za kuma mu zauna gobe da kuma jibi insha Allah. Jibi za mu yi Nahajul Balagha, don shi ma karatu ne. Amma bayan Nahajul Balagha din, sai mu dora wani abu dangane da Sayyida Zahara din har ya zuwa dare, insha Allah. Da wasu addu'o'i. Yanzu saboda ainihin, ni na san ku ba ku gaji ba, amma muna då gajiya tare da mu, saboda haka dole za mu dan takaita a daidai wannan lokaci,
ya zama mun dan yi shimfida. Insha Allah daidai gwargwado a wannan dan lokacin (in zai yiwu) za mu yi kokari mu karanto ba'adin Hadisan Sayyida. Musamman 'Fadakiyya' wanda ya shafi wafatinta. Wanda a bara mun karanta a cikin Jimada Assaniya Fadakiyya, za mu yi kokari mu karanto daidai gwargwado, da waki'ar abin da ya faru da ita bayan wafatin Mahaifinta, har ya zuwa nata wafati din a gurguje. Da wadannan kwanakin da kuma na masu zuwa insha Allahul Azeem.
Muna fatan Allah (T) ya buda ainihin zukatanmu da kwakwalenmu da idanunmu da kunnuwanmu ga ganin gaskiya da jin ta da fahimtar ta. Kuma muna rokon Allah (T) ya ba mu ikon bi. Don fahimtar gaskiya wani abu ne daban, bi kuma wani abu ne daban. Na farko dai ma ya zama ka ji din Shi ma baiwa ne. Mun gode ma Allah (T) da ya sa ainihin da ya zama al'amari bai zama rufe gare mu ba, har ya zuwa karewar wafatinmu. Muna fata Allah ya sa mu a cikin jimlar wadanda zai yi amfani da su wajen bayyanar da gaskiya da tabbatar ta.
Tags
Munasaba