Offline

YANZU NE HANKULAN MUTANE YA ZO GA ABIN DA MUKE CEWA:

To bayan jaje kuma har ila yau, da yake mun gwama zama da Mawallafa da Mawaka, sun yi kama ko? Duk talifi suke yi, wannan yana yin nizami, wannan yana zube. Da mai zube ne da me wake ko? Ko da yake Mawallafa ma za su iya wallafa wakoki ai, duk da yake masu talifin abubuwan da suke talifi ba wai ‘generally’ bane, talifin (‘ideology’ din Harka ne musamman. 

Ana kokarin a fidda ‘ideology’ din Harka ne, kiran da ake yi me ake cewa? Domin musamman ma lokacin da waki’a ta auku, lokacin ne hankulan mutane (ya karkato garemu). Har a kasan nan, abin ban mamaki, shekararmu 40 cur kafin su dira mana muna harkokinmu, amma wani sai ka ga ya yi garau wai bai ji ba.

To, nima na sha mamaki, lokacin ina tsare a gidan yarin Kaduna, wani cikin ma’aikatan gidan yace, to nan wani ya yi kira ga a yi ‘revolution’ amma ba a bashi hadin kai ba. Ya fadi wani mutum. Lokacin Buhari din nan. Yace nan ya yi kira ga ‘revolution’ amma ba a bashi hadin kai ba, ‘revolution’ ya kamata a yi a kasar nan.

Na yi shiruuu, nace yanzu wannan yana nufin duk shekara 40 shi bai ji komai (na Da’awarmu) ba? Kuma duka-duka dan shekara 40 da wani abu ne, an fara da’awar yana karami ne, amma shi wala’alla bai taba ji ba.

Wani kuma cikin ma’aikatan ina masa magana, sai nace ai ma’anar Shi’a shine “Shi’atu Ahlulbait” a takaice, wato magoya bayan Iyalan gidan Annabi (S). Sai mutumin ya yi shiru, yace tunda yake bait aba jin wannan ba, ashe ma’anar kalmar kenan?

Nace o’o! Dan Adam kuma sai dai ka ganshi. To shi yana wace duniyar ne ni ban sani ba? Ko bai damu bane da ya je ya sani? Baka dai da yadda za ka yi da mutane wani lokaci, ko basu so su sani ne? Amma dai ya kamata abin ya zama ya je gare su ne. Ta yadda zai zama idan ma bai ga damar ya sanin ba, to ba mu ne muka kasa isar masa da sakon ba.

To daidai gwargwado bayan da waki’ar nan ta auku ne sannan mutane hankalinsu ya fara zuwa kanmu, suna son su an su wane ne? me ake cewa ne? sannan suka fara bibiya. 

MAKIYA SUN SO NUNA MU A MUMMUNAN KAMA:

Kuma da can, da ma yanzu lokacin da suka dira mana sun yi kokarin su ba da wani irin sura tamu wata iri daban a fuskar mutane. Da yake ta Allah ba tasu ba, sai basu iya ba da surar da suka so su bada a kanmu ba.

Sun so su nuna kamar suna hulda ne da wasu dodonni, ka san dodo, ba wanda ya ga dodo, ana dai maganar dodo ne kawai. Kowa idan aka ce dodo a Hausa ya san abin tsoro ne kawai, ko da bai taba ganinsa ba, in aka ce ga dodo nan baka san shi ba, amma ka san abin tsoro ne dai ko? Da za a ce ga dodo nan, ai ka san kowa zai zuba a guje ne ko? Saboda tsoronsa yake yi. A tatsuniyoyi ana ta labarin dodonni, har a kan ce suna cin mutane. Ka ga dodo kuwa lallai abin gudu ne. (Dariya).

To, sai ana kokarin a nuna ‘yan uwa a wasu dodonni ne wadanda kowa ya kama ya ji tsoronsu, ya yi nesa da su, kuma ya kamata a kawar da su ne in ba haka ba za su jagula al’ummar nan, za su janyo al’umma ta fada cikin mummunan hali, za su kawo wani irin salo na addini wanda ake kyamar kowane mutum in ba irin nasu ba, za su karkashe mutane ne, su yamutsa komai su sa mutane, su sa kowa ya rika tafiya da hannu ya daga kafafunsa sama, ko ya rika tsallen kwado da ka. Ace abin da za su yi kenan. Ko kuma za su tsinko taurari ne ma su runtime da su kasa, duk komai ya rugurguje dai. Wato abin tsoro dai. 

Lokacin waki’ar Abacha sun yi haka nan, suka rika nuna mu kamar ma mun sakko ne daga sama, kamar dama bamu a doron kasa, kamar wasu mutane ne da yanzu suka bayyana, ko sun fito ne daga kasa, ko ruwa ne ya yi ambaliya aka same su, ko kuma sun faffado ne daga sama? Kawai gasu nan dai. Aka dinga nuna mu a matsayin wani abu daban. Sai da Abacha ya yi kan kowa, sannan sai suka dawo suka canza luga.

To, haka ma wannan suka zo suna ta kokarin su nuna ai wadannan wasu dodonni ne. don haka ma lokacin da suka ce wai sun kai mu kotu, mu ba muna zuwa kotun bane amma sai su yamtsa garin lokacin da za a shiga kotu, duk wai suna ba da tsaro ne. Ka san za a kai dodo (kamar yadda suke kokarin nuna mu) kotu, ka san dole ka dauki mataki, in ba haka ba mutane ba za su zauna lafiya ba, in dodon nan ya fito zai kamface su ne kila. Saboda haka sai duk su yamutsa gari wai suna ba da tsaro.

To, duk ba da tsoro ne kawai, amma sai ya zama ta Allah ba tasu ba, sam basu ba kowa tsoro ba. Sai ya zama ma sun yada abin ne, musamman a idon duniya, sauran mutanen duniya kuma sai kowa ya nemi ya san mene ne game da wannan abin.

TARUKANMU SU KAN ZAMA KAMAR IMU-IMU NE:

To, a daidai wannan lokacin muke tunanin ya kamata a ba (isar da sakon) muhimmanci. Tunda muna yin magana ne, galiba tun saba’inonin nan zuwa farkon tamaninonin nan na lura da cewa muna magana da kanmu ne, duk lokacin da muka yi wata munasaba sai kaga yamu-yamu ne muka hadu, mu ke magananmu mu ke jin abinmu, sauran mutane basu san abin da muke cewa ba, in za su wuce aka ga taro sai su ce ai dalibai ne suke taro, yanzu kuma sai aka dawo Shi’a ne suke taro, shikenan sai ka wuce tunda kai ba Shi’a bane.

Da can, shekara 40 da ‘yan kai kai ba dalibi bane, tunda kai ba ‘student’ bane ba ruwanka, sai ka wuce. Yanzu kuma kai Shi’a ne? A’a, sai ka wuce, baka san ma me suke cewa ba, sai su yi magana da kansu. Wato muna magana da kanmu ne. Jawabanmu da muke yi mu muke sauraron abinmu.

Na san na kan rika ma wasu mutane shagube da cewa to ni ban ga amfanin wa’azinku da kuke yi ba. Kun san wasu mutane ‘yan dirkaniya masu wa’azin kasa baki daya? Akwai lokacin da suka je wani gari mutanen garin suka fita gaba daya, suka daure awakinsu a gidajensu, suka rufe kajinsu a akurki suka fita suka bar garin, sai da wadannan suka zo suka gama wa’azinsu suka fita sannan mutanen garin suka dawo.

To kuma wa’azin nasu bai da wani amfani, saboda mene? Duk wanda suka tara mai ra’ayi irin nasu ne. Sai su ce wadancan mutanen kafirai ne, mushirikai, ‘yan wuta. To, kuma duk cikansu nan su babu kafiri ko mushiriki dan wuta, duk ‘yan Aljanna ne. Suka rika cewa wadancan kun ga addinin da suke yi ba daidai bane, ‘yan wuta ne. 

To, tunda ka tara mutanen da ba dan wuta a cikinsu, kana magana da wani zai shiga wuta kuma shi bai zo ya ji wa’azin ba ballantana ya ji tsoro, to mene ne amfanin wa’azin naka? To, haka nan su kan yi, su su yi magana da kansu, su tara mutanensu su yi ta fada musu abin da suke fadawa wasu, su kuma su ji abinsu.

AKWAI BUKATAR A RIKA TARJAMA SAKONNI ZUWA YARURRUKA:

Nake cewa to, yanzu sun bude kunnuwa da idanuwan mutane, abubuwan da suke yi (mana) sun sa dole mutum ya rika cewa wai wadannan wadanne irin mutane ne? To, sai ya nemi ya sani. Lokacin aikin isar da sako kenan, musamman da harsunan da suke fahimta. 

Don galiba muna magana da harshen Hausa ne, saboda haka akwai bukatar ya zama akwai wadansu abubuwa da aka mai da harsunan da mutane za su fahimta, musamman a nan harshen Ingilishi, mutane suna fahimtar harshen Ingilishi din, in aka mai da abubuwa aka yi tarjamarsu da Ingilishi.

Na san a baya can an yi yunkurin tarjamar Ingilishi din, har sai nake cewa amma a rika lura, idan ana tarjama akwai bukatar a lura da dawa ake magana? Saboda da yawa idan ina magana na kan yi la’akari da wadanda suke gabana ne, saboda da su nake magana.

A lokacin da nake tsare, wancan karon ba wannan ba, ina jin ko 1997 ne, aka yi wata jarida mai suna Pointer, to shikenan sai na ga ta yi tarjaman wata magana da na yi a kauye. Ni ina tunanin kwakwalen mutanen kauyen ne, kuma na yi musu magana da harshen da za su iya fahimta da Hausa, to sai aka dauka aka mai da shi Ingilishi. Hankalina kuwa ya tashi, don bai dace ma wani mai karatun Ingilishi ya ji wannan maganar ba sam, saboda ba da shi aka yi magana ba. 

To ina cewa a rika lura da abin da za a tarjama ya zama ya yi daidai da wanda ke fahimtar Ingilishi din ne. Kuma tunda muna ma da wadansu materials da yawa na Ingilishi, kun san akwai bambanci tsakanin rubutu da magana, in mutum yana magana ya kan ta maimaita kansa ma domin ya sa abin a ji shi sosai, to amma in ka zo kana rubutu ba za ka dinga maimaita maganar ba. 

Wani lokaci kuma zai yi wata magana kalmomin ba su cika ba, sai wanda ya iya harshen sosai ya ciccika masa. Sai ya mai da jimlolin su zama daidai. Ko da yake idan zai cika masa zai yi kokari ya saka ko a ‘bracket’ haka, don a gane bambanci tsakanin maganar mai rubutu da maganar wanda ya fada, ko da ya zama akwai kuskure a rubutun sai ya zama na mai rubutun ne ba na mai maganar ba, amma yana kokarin ya kai wannan ra’ayin ne.

To sai nake ganin idan aka yi magana da Ingilishi, shi ya fi dacewa a maishe shi Ingilishi, an fahimta ai? In aka yi magana da Hausa kuma a saka shi da Hausa. Idan kuwa aka yi magana da Hausa ana neman a maishe shi Ingilishi to ya kamata a yi la’akari da mai fahimtar Ingilishi ne ya zai gane wannan abin da aka fada. Haka nan kuma idan maganar da Ingilishi ne ana so a maishe da shi Hausa, dole a yi la’akari da shi kuma mai fahimtar Hausa ya zai fahimce shi? An fahimta ai. To akwai wannan.

JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) GA ‘YAN CIBIYAR WALLAFA DA MAWAKA (2)
Za mu cigaba.

— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)
www.cibiyarwallafa.org

Post a Comment

Previous Post Next Post