Saboda haka yanzu lokaci ne da su kuma Mawakanmu za su iya tallata wadannan abubuwan (Harka za Mazlumiyyarta) kenan. Ba da sunan suna musu raddi ba, a’a (da sunan) suna isar da sakon. Kowane abu ya zama an isar da sakon shi a wake, ta yadda mutane za su saurare shi cikin sauki su ji duk abin da ake so a fada din, amma a nizamance.
To, ba shakka an yi wakoki daban-daban, har ma mun rika sauraronsu muna tsare, muna tsare mun rika sauraron wakoki a DVD, ko da yake yanzu DVD din nawa an batar min da Memories din, sai dai ina sauraron wanda aka sajjala a Telegram.
Lokacin waki’a din nan an yi wakoki daban-daban da suka isar da sakonni daban-daban a munasabobi daban-daban, ka,ar yadda nace Alhamudilillah daidai gwargwado an yi. Ban san tasirinsu a sauran mutane ba, ku ne za ku iya fada min, amma a ‘yan uwa kam za a iya saninsa cikin sauki. Amma ban san tasirinsa a sauran mutane ba.
Haka ma kazalika Talifan da ‘yan uwa ke yi, ina ganin kamar daidai wannan lokacin ne nake cewa ya kamata a kai sakon. To ban san shima izuwa wane mikidari ne sakonnin nan ke isa ga mutane ba, don da yawan mutane suna son su ga wani abu a rubuce, sun so su ji wani abu, har su kan ce wai ina shi littafin da shi Malam ya rubuta? Ko wani abu mai kama da hakan. Ya zama an same su irin wadannan.
Ban san tasirinsu ba, ku za ku bani labari, tunda kuna waje, mai yiwuwa kun ji tasirin irin wadannan abubuwan na hanyoyin isar da sakon izuwa ga al’umma. Amma mun san cewa lallai abin a waje duk da ba sun iya Hausa bane, al’amarin waki’ar nan ya tambatsa al’amarin nan a sauran duniya, sosai sosai, fiye da kima.
Wasu kamar Indiyawan nan suna ta magana da harshensu, suna ta bayani, suna kuma tarurruka, za ka ga Malamansu suna ta bayanai da harshensu kai baka ma san me suke cewa ba, ka ji wasu sun ce Zakzaky in sun iya, wasu kuma su ce Zak-zaki, haka nan ka ji su iri-iri ana ta magana sai dai ka ji, har da wake ma sun yi. Wasu Indiyawa ma sun yi wake, sun yi wakoki da harshensu.
MUNA SO MU KARFAFA GUIWA NE:
To, shima ka ga irin wannan hanyoyin isar da sako kam lallai sai mu ce daidai gwargwado an isar. Abin da muke so a karfafa guiwa ne, shi yasa ma dalilin da ya sa muka ce (a zo). An yi ta ‘booking’ batun ‘yan CIBIYAR WALLAFA, muna cewa to a dakata dai, akwai gungun mutane daban-daban da muke so ya zama an basu dama.
Kullum a kan dan ba wasu gungun mutane (dama), ko da yake ba kowanne ne ake ganinshi a labarai ba, wani ba a daukan hoto ba ma a daukan sauti, haka mu kan zo mu yi zamanmu ba a ma ji ba. Wasu ne ake gani.
To, mun zauna da gungun mutane daban-daban, ko yanzu ma akwai batun a wannan makon za mu zauna da Sharifai, kuma karshen makon za mu zauna da wadanda aka ji ma rauni. Haka nan dai za mu dan zauna da ba’adin mutane haka nan. Kuma iyalan Shahidai suma mun yi kashi na biyu, kuma dai ba an gama bane, za a debo wasu kashi na uku da na hudu daidai gwargwado tunda dai ba an gama bane, tunda yake yanayi din ba zai bamu dama a gana da kowa da kowa a lokaci guda ba, ko yanzu nan an tsittsinto wasu ne a madadin saura, kuma mun san insha Allah idan kuka je za ku isar da sako ga sauran da ba a basu daman zuwa ba, don ba zan ce basu samu damar zuwa ba, ba a basu daman zuwa bane, da an basu dama za su zo.
YANAYIN KASA YA MAI DA TAFIYA WAHALA:
Na san yanayin da kasar ta shiga ya mai da tafiye-tafiye na da wahala, har ma lokacin da muke magana nake cewa wannan za mu iya baku wannan kurarren lokacin? Ranar Laraba muka yi maganar, har nace ai lokacin ya kure. Aka ce ai kowa yana da shauki. Nace ai tafiyar kuma da wahala ba irin da bane da ko da gobe ne sai a ce jama’a su zo, goben za su zo. Kuma yanzun nan za su zo.
Lokacin da yan uwa suke zuwa in za a yi munasaba, kamar munasabobin nan da muke yi a Zariya, sai ka ga wasu su kan taso a mota daga Lagos da yamma bayan Magriba, su iso da sassafe, suna zuwa su wuce wajen ‘program’ in an tashi su kama hanya. Wasu suna yin haka nan. garuruwa daban-daban, sai su shirya yadda in sun taso isowarsu zai yi daidai da safe ne, sai kawai su je wajen faretin, in an gama su kama hanya su koma. To yanzu ba zai yiwu ba, kun ga yadda dai kasa kowa ya riga ya san yadda ta kasance.
KISAN DA AKA MANA BA BISA KA’IDAR SHARI’A BANE:
Kuma har yanzu muna ta tambaya, wai su mutane basu gane cewa duk musibobin nan musabbabinsu shine abin da aka aikata a Zariya ba? Na tambayi wani babba ne a cikin jami’ansu, sai yace suna ganewa, yace suna fada ‘in private’. Nace da ban mamaki, amma na ga har yanzu basu dandara ba.
To, sauran mutane kuma har yanzu daga mai gum da baki, galiba masu gum da baki ne, amma wasu suna dan guna-guni a gefe. Amma dai sai na ga cewa suna maganar halin da kasa ta shiga da abin da ake ma mutane, amma kuma suna ganin abin da aka mana wai daidai ne. Amma da ban mamaki.
Sai su ce kai wannan gwamnati tana kashe mutane, sai ka ga suna ta mita ana kashe mutane, har da kona mutane, da sauransu. In wani yace haka suka yi ma Shi’a a Zariya, sai su fara cewa ai daidai ne. To, in kuwa har kisan wani daidai ne ai na wani ma daidai ne. Kisan kai kisan kai ne ai ko? Ka taba ganin kisan kai kace na wannan ya yi daidai? A yi kisan kai, barna, a kashe mutane maza da mata da yara kace ya yi daidai? A ina?
Har nake cewa wannan in kace addini ne, sai mu ce to sai dai ka fada mana wane addini ne, amma ba addinin da Manzon Rahma (S) ya zo da shi ba. Ba addinin Manzon Rahma (S) bane, wanda yace “Babu mai yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta.” Hatta Kunama an hana ka kashe ta da wuta. Kana iya kashe kunama, amma kar ka kona ta, ko Maciji, kar ka dauki maciji ka saka shi a wuta. Ba mai azaba da wuta sai Ubangijin wuta, haramun ne, bamu da hukuncin kona mutum da wuta.
To kuma kisa ana yi ne ta hanyar yanke hukuncin shari’a. Ba a taba sanin ana zuwa a samu gari a kashe kowa da kowa maza da mata ba. In shari’a ta samu mutum da laifi cewa shi ya cancanci a kashe shi saboda dalilai na shari’a, to tana yanke masa hukunci ne. Har ma in dalilin ya yi kisan kai ne, sai an bashi dama an dinga tattaunawa, an tabbatar da cewa babu wata fatawa face mutumin nan kashe shi za a yi, saboda abin da ya cancance shi kenan.
Amma in wani abu ne kamar yadda suke cewa babin Ridda, ai yana da wahala. Su Malamai suna jin tsoron shiga wannan ‘area’ din, har aka ce su Malamai wadanda suka kai martaban Maraji’ai sai sun yi ittifaki a kan haka nan kafin a zartar da hukunci din. Idan Malami goma (suka hadu), tara suka ce a kashe, daya yace bai kamata a kashe ba, to dole ne a saurara.
Amma wannan ban taba sanin hukuncin da in za a kashe mutum har wala yau hukuncin ya yarda a kashe ‘ya’yansa ba, su kuma suka yi laifin mene? Ba a kashe mace mai ciki, ko da shari’a tace a kashe ta in tana da ciki ba a kashe ta. Ba a kashe mace mai shayarwa, ko da shari’a ta kashe ta, sai ta yaye danta.
Mu kaddara shari’a yanzu ta yanke mata hukuncin kisa amma tana da ciki, to ba za a kashe ta da cikin ba, saboda shin a cikin bai yi laifin komai ba. In kuma ta haihu sai an bata damar ta yaye yaron, har ma aka ce ba yaye kawai ba ma har sai ya yi famfara – ma’ana ya zubar da hakoran farko ya yi na biyu, yanzu zai iya cin abinci, kakkarfa ne, sannan a ce to shikenan. In ta kama ita za a kashe ta kenan bisa ka’idar shari’a.
Amma wannan mata da jarirai, da mata masu ciki, duk suka karkashe, wani kuma ya zo yace wai addini ne. To wannan addinin, sai dai kai idan kana da naka addinin ne na daban, amma dai ba addinin da Manzon Allah (S) ya zo da shi ba, sai dai in wani addinin ne kake yi daban.
To, sun yi abin da suka yi, kuma suna ganin jaza’i, amma sun kasa ganewa. Kuma har yanzu, idan mutum ya yi laifi yana ganin ai laifinsa daidai ne, ai kaga da sauranshi ko? A yi irin wannan abu ace kuma wai abin da aka yi daidai ne, kuma ba a tunanin wani abu, har ma ana tunanin za a cigaba da karawa, to shikenan ku ba da kokari. Allah ba azzalumin kowa bane, saura jaza’i insha Allah, kun fara gani ma kenan. Jaza’o’i iri-iri.
To, insha Allah da yake akwai Mawallafa da Mawaka, kowanne za mu basu dama, ai magana da yawun Mawallafa.
JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) GA ‘YAN CIBIYAR WALLAFA DA MAWAKA (4)
Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)
www.cibiyarwallafa.org
Tags
Jawaban Jagora